Kisar Ƴan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu

Kisar Ƴan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu

  • Mazauna garin Akpawfu a karamar hukumar Nkanu ta Gabas ta jihar Enugu sunyi kaura daga garin
  • Hakan ya biyo bayan dakarun sojoji fiye da 40 da suka iso garin cikin motocci bayan kashe yan sanda a garin
  • Wasu mazauna garin sun ce sojojin na zargin yan bindigan suna samun mafaka a garin ne hakan yasa suke bincika wasu gidaje

Mafi yawancin mazauna garin Akpawfu da ke karamar hukumar Nkanu ta Gabas sun tsere daga gidajensu, wadanda suka yi saura suna zaman dar-dar a yayin da sojojin 82 Division ta Rundunar Sojojin Nigeria, Enugu suka shiga garin.

Wakilin Daily Trust ya gano cewa akwai yiwuwar sojojin su kama maza da matasa a garin saboda kashe wasu yan sanda da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai wa hari.

Sojojin da adadinsu ya dara 40 sun isa garin cikin motocci masu bindiga da wasu motoccin na jami'an tsarokamar yadda Daily Trust ta rueaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

Kisar 'Yan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu
Kisar 'Yan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar majiyoyi, sojojin suna ikirarin cewa mazauna garin ne suka bawa yan bindigan mafaka.

Yan bindigan da suka kaiwa yan sandan hari, sun shigo garin ne daga Akpugo, daya daga cikin motarsa ya yi kundun bala ya kone kusa da cocin St Philip Catholic Church da ke Akpawfu.

Majiyar ta ce:

"Sojojin suna tunanin yan bindigan sun kona motarsu ne da kansu saboda badda-kama, kuma suna tunanin akwai yiwuwar suna nan sun boye a garin."

Daily Trust ta tattaro cewa isar sojojin garin ya saka mutane da dama barin gidajensu.

Wani mazaunin garin da baya son a ambaci sunansa ya ce:

"A yanzu da nake maka magana, dukkan matasa maza har ma da mata sun boye a yayin da sojojin ke ikirarin bincikar gidajen da ake boye yan bindigan.
"Ni dai ban san ko da gaske bane. Abin da na sani shine yan bindiga sun wuce ta garin mu zuwa Abakaliki. Ban fahimci abin da yasa sojoji ke hukunta mu ba.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Bayan Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga a Zamfara

"Matasan mu suna tserewa wasu garuruwan domin mun san cewa sojojin za su rika zargins da aikata laifin."

An yi kokarin ji ta bakin direktan hulda da jama'a na 82 DV, Enugu, Kwanel Abubakar Abdullahi amma ba a yi nasara ba don bai daga wayar ba.

Bai kuma amsa sakon kar ta kwana da aka yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

A wani labarin daban, Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel