'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki garin Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara
  • A yayin farmakin, sun sheke 'yan sa kai bakwai yayin da suka bankawa motar yaki ta sojoji 1 wuta
  • An gano cewa sun kai mugun harin ne a cikin dare wurin karfe 3 amma 'yan sa kai suka fito domin baiwa jama'a kariya

Maru, Zamfara

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe 'yan sa kai 7 a wani hari da suka kai garin Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa miyagun 'yan bindiga sun kutsa yankin wurin karfe 3 na dare kuma sun je wuraren da suka yi niyya.

KU KARANTA: Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta
'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

Sun dinga harbi a iska kuma daga nan suka shiga wasu gidaje kuma suka kwashe mutane 13 da suka hada da mata.

"Wadanda aka kashe sun hada da 'yan sa kai wadanda cike da zakakuranci suka fito daga gidajensu domin fada da maharan. 'Yan bindigan daga nan suka bankawa motar yaki wuta.

“Jami'an tsaron sun yi martani amma sai aka ci galabarsu sakamakon yawan 'yan bindigan da suka bayyana," wani mazauni yankin yace.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Garin Dansadau yana nan a nisan kilomita dari daga kudancin garin Gusau, babbar birnin jihar.

Miyagun 'yan bindigan sun yanke hukuncin kai mummunan harin ne bayan 'yan sa kai sun dinga kashe wadanda ake zargi da zama 'yan bindiga a watannin da suka gabata.

Mazaunan yankin sun hana 'yan bindiga samun abinci da suka hada da biredi da ruwan lemo daga 'yan kasuwar yankin.

'Yan bindigan wadanda a bayyane suka fusata da mazauna yankin, sun fara kaiwa manoma harin daukar fansa.

Kara karanta wannan

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

An halaka manoma masu tarin yawa tare da sace wasu tun farkon wannan shekarar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, bai tofa albarkacin bakinsa ba saboda ba a samesa ba har yayin rubuta wannan rahoton.

A wani labari na daban, mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya gurfana a gaban wata kotun daukaka kara ta Kwatano saboda matsalar da ta hada da hukumar shige da ficen kasar.

Kotun ta bukaci a cigaba da tsare mata Igboho a yayin da za ta cigaba da sauraron karar a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma, matarsa, Ropo, wacce 'yar asalin kasar Jamus ce an saketa domin kotun tace bata kama ta da wani laifi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng