Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu
- Wasu yan bindiga sun kai hari a shingen yan sanda da ke Obeagu-Amechi a karamar hukumar Enugu ta Kudu
- Yan sanda sun tafka gumurzu da yan bindigan inda aka kashe a kalla mutum hudu daga bangaren yan sanda da yan bindigan
- Rundunar yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da afkuwar harin amma bata bada cikakken bayani ba a yanzu
A kalla yan sanda hudu ne da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka mutu a ranar Laraba yayin da wasu yan bindiga suka kai hari shingen yan sanda a Obeagu-Amechi a karamar hukumar Enugu ta Kudu, Daily Trust ta ruwaito.
Baya ga jami'an tsaron, mazauna gari da mutane da ke wucewa sun rasu, wasu kuma sun jikkata sakamakon harsashin bindiga yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da yan bindiga.
Daily Trust ta ruwaito cewa yan sanda sun dakile harin, duk da cewa an rasa mutane a dukkan bangarorin biyu.
Wasu shaidun gani da ido sun ce an kai harin ne a wani fitaccen wuri mai suna Mmiri Ocha Amodu tun misalin karfe 5.30 na yamma a ranar Laraba har zuwa karfe 7 na yamma.
Wani da ya nemi a boye sunansa, ya ce ya gano yan sanda hudu, fasto daya da wani mai gadi daya cikin wadanda suka mutu kuma an kai su wurin ajiye gawa a asibitin koyarwa ta Jami'ar Nigeria ta Ituku a Ozalla.
Majiyar ta ce:
"An tafka gumurzu tsakanin yan sanda da yan bindiga.
"Mutane sun shiga firgici sakamakon musayar wutar suna neman tsira da ransu.
"Ba mu taba ganin irin wannan lamarin ba a unguwar mu. Ya faru ne a Obeagu – Amechi zuwa Agbani Nkanu kilomita kadan daga Enugu babban birnin jihar Enugu."
Majiyar ya kara da cewa yan sandan Amagunze sun tare maharan sun bindige su a yayin da suke kokarin tserewa amma an kuma kona motar sintirin yan sanda.
'Yan sanda sun tabbatar da harin
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu.
Ndukwe ya ce:
"Har yanzu muna kan tattara bayanai game da harbe-harben da aka yi a yammacin ranar 21/07/2021, inda aka kaiwa yan sanda hari a shinge da ke Obeagu-Amechi a karamar hukumar Enugu da Amagunze a karamar hukumar Nkanu."
Ya ce an fara bincike kan lamarin kuma zai kara bada bayani nan gaba.
Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe
A wani labarin daban, jami'an tsaro sun dakile wani gari da aka yi niyyar kaiwa a garin Geidam a jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mayakan Boko, wanda suka kai mummunan hari a Geidam watanni da suka gabata sun sake yunkurin kai hari a gari a yammacin ranar Laraba.
Modu Ali, wani mazaunin garin na Geidam ya ce an tsegunta wa jami'an tsaron cewa yan ta'addan za su kawo harin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng