'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

  • Yan fashi da makami sun halaka mukaddashin kwamandan 196 Battalion ta sojojin Nigeria, Manjo MS Sama'ila
  • Manjo MS Sama'ila ya rasu ne sakamakon harbin bindiga da yan fashin suka masa tare da mai tsaronsa a Dundubus
  • Sai dai mai tsaronsa Alisu Aliyu shi bai mutu ba duk da harbin da aka masa yana asibitin Shekoni a Dutse ana masa magani

Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Dakarun sojojin Nigeria
Dakarun sojojin Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Sanarwar ta rundunar sojojin ta fitar ta ce:

"Misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar 2 ga watan Yulin 2021, Ƴan fashi sun kai wa wani Manjo MS Sama'ila, muƙadasshin kwamandan 196Bn a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa 20NA/79/4559 LCpl Alisu Aliyu hari a Dundubus."
"An bindige jami'in har lahira, yayin da mai tsaronsa, ya samu raunin bindiga. An kai gawar jam'in asibitin Shekoni a Dutse. Sojan na karbar magani shi kuma."

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Dakarun sojojin Nigeria na Sector 1 Operation Hadin Kai (OPHK) tare da taimakon Yan Sa-Kai na Civilian JTF, a ranar 3 ga watan Yuli sun kama wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram biyu, Premium Times ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce sojojin sun kama wasu kayayyaki da aka siyo domin kaiwa yan ta'addan.

Mr Nwachukwu ya ce sun kama gurneti na hannu, diga daya, mota daya, kekuna biyar, wayoyin salula biyu (Tecno da Infinix), man fetur da man juye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: