'Yan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Bayan Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga a Zamfara

'Yan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Bayan Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga a Zamfara

  • Yan sanda a jihar Zamfara sun tafka gumurzu da yan bindiga a hanyar Gusau zuwa Sokoto
  • Yan bindigan sun tare hanyar ne suna yi wa matafiya fashi tare da sace wasu daga cikinsu don karbar kudin fansa
  • Yan sandan sun isa wurin da yan bindiga suke, suka halaka guda suka ceto mutum 11 bayan musayar wuta

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kashe wani hatsabibin dan bindiga a jihar sannan ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis a Gusau.

'Yan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Bayan Fafatawa Da 'Yan Bindiga a Zamfara
Jami'an Yan sandan Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

Shehu ya ce:

"Jiya misalin karfe 1 na rana, yan bindiga da dama sun tare hanyar Gusau zuwa Sokoto a kusa da Dogon Karfe hakan yasa matafiya suka rika neman tsira.
"Cikin kankanin lokaci jami'a yan sanda da ke sintiri a hanyar suka nufi wurin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

"Da isarsu wurin, yan bindigan suka fara harbi bayan sun riga sun kama mutane suna shirin shiga da su daji.
"Jami'an yan sandan sunyi nasara kan yan bindigan, hakan ya hana miyagun cigaba da zaluntar matafiya."

Ya bayyana cewa yayin artabun an kashe dan bindiga daya kuma nan take aka ceto mutum 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa:

"Rundunar na tsananta bincike domin ceto sauran wadanda aka sace din da yan bindigan suka shigar da su daji kafin su iso.
"An sada dukkan mutanen da aka ceto da iyalansu."

Har wa yau, ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Hussaini Rabiu, ya jadadda aniyarsa na ganin an kawo karshen kallubalen tsaro a jihar.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel