Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

  • Ambaliyar ruwa sanadiyyar ruwa mai ƙarfi ya laƙume rayukan yan mata biyu tare da dabbobi sama da 140
  • Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ja'oje dake ƙaramar hukumar Wamakko, inda gidaje dama suka rushe
  • Shugaban sashin jin ƙai na hukumar SEMA ya ce akwai sauran ƙauyuka biyu da abun ya shafa

Wasu yan mata biyu kuma yan uwan juna sun rasa rayuwarsu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ƙauyen Ja'oje dake ƙaramar hukumar Wamakko, jihar Sokoto, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kuɓutar da Wani Yaro da Aka Sace a Cikin Akwatin Gawa

Hamida da Maryam sun rasa rayuwarsu ne bayan ɗakin da suke bacci ya faɗa musu sanadiyyar tsananin ruwan sama da ake yi.

An yi ambaliyar ruwa a jihar Sokoto
Ambaliyar Ruwa Ta Lakume Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban sashen jin ƙai na na hukumar bada taimakon gaggawa (SEMA), Mustapha Umar, ya bayyana cewa ambaliyar ta laƙume dabbobi aƙalla 144.

Gidaje da dama sun rushe

Umar ya ƙara da cewa ambaliyar ta shafi gidaje da dama, domin lamarin ya shafi magidanta kimanin 177.

Yace: "Haɗakar jami'an hukumar bada agaji ta jihar Sokoto (SEMA), hukumar ta ƙasa (NEMA), da kuma wasu ƙungiyoyi sun dira ƙauyen domin duba irin asarar da aka yi."

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan

Ya kuma ƙara da cewa akwai wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar da ambaliyar ruwan ya shafa, amma har yanzun ba'a tabbatar da yadda lamarin yayi a yankunan ba.

A wani labarin kuma Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno

Aƙalla mata 10 waɗanda mafi yawan su masu juna biyu ko masu shayarwa ne suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin karbar abinci a Monguno, jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa matan sun rasa rayukansu ne a turmutsutsin karɓar abincin da zasu ci a sansanin yan gudun hijira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel