'Karfin Hali: Ƴan Bindiga Sun Fara Rubutawa Mutane Wasika Kafin Su Kawo Hari a Sokoto
- Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto, Sa'idu Ibrahim ya koka kan yadda yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a ƙauyukan jihar
- Ɗan majalisar mai wakilar Sabon Birni ta Kudu ya ce lamarin ya kai ga har wasika ƴan bindiga ke rubutawa kafin su kawo hari
- Ɗan majalisar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jiha su ƙaro adadin jami'an tsaro tare da taimakawa ƴan banga da makamai na zamani
Sa'idu Ibrahim, ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto, ya ce a yanzu ƴan bindiga na rubutawa mutanen ƙauyuka wasika kafin su kawo musu hari, The Cable ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke magana game da harin da yan bindiga suka kai ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar.
DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari
'Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto, sun kashe sojoji biyu sun raunata 7, sun sace mutane da dabobi
Ibrahim, wanda ke wakiltar Sabon Birni ta Kudu a Majalisar Jihar, ya bukaci gwamnatin tarayya da jihar su gaggauta ɗaukan matakan dakile hare-haren kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A cewar kamfanin dillancin labarai ta NAN, ya ce lamarin ya jefa mazauna ƙauyukan cikin matsaloli duba da yadda yan bindigan ke adabarsu da hari inda ake rasa rayuka da dukiyoyi.
Ya ce:
"A yau mutane da ƙauyuka fiye da 500 a ƙaramar hukumar Sabon Birni, amma a yanzu da nake magana ƙauye ɗaya ne tak ƴan bindiga ba su kaiwa hari ba."
"Sakamakon haka, kimanin kashi 35 zuwa 40 na mutane ƙauyukan sun koma hedkwatar karamar hukumar domin tsaro.
"Lamarin na cigaba da zama matsala ga rayuwan mazauna ƙauyukan, yayin da yan bindigan na cigaba da kai hare-haren ba tare da tsoron jami'an tsaro ba.
"Duk lokacin da yan bindigan za su kawo hari ƙauyukan, saboda ƙarfin hali har wasika suke rubutawa mutanen kafin su kawo harin."
Dan Majalisar Ya Bukaci Gwamnati Ta Karo Jami'an Tsaro
Ya koka game da rashin isasun jami'an tsaro yana mai cewa ƴan bindiga sukan zo ne da yawa sosai.
KU KARANTA: IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu
Duk da hakan ya yabawa jami'an tsaron da ake turawa yankin saboda jajircewarsu wurin aiki yana mai kira a ƙaro wasu domin magance matsalar.
Ibrahim ya kuma shawarci gwamnatin jihar ta taimakawa ƴan banga da makamai na zamani domin su rika taimakawa ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi a yankunan.
'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa
A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.
Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.
Asali: Legit.ng