Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kuɓutar da Wani Yaro da Aka Sace a Cikin Akwatin Gawa
- Jami'an tsaron hukumar shige da fice sun samu nasarar kuɓutar da wani yaro ɗan shekara 12 a cikin akwatin gawa
- Mutanen da suka yi ƙoƙarin sace yaron sun saka shi cikin akwatin gawa kuma sanye da fararen kaya
- Bincike ya nuna wanda aka kuɓutar ɗin ɗan asalin jamhuriyar Benin ne, kuma an miƙa wa yan sandan ƙasar
Jami'an shige da fice (NIS) sun kuɓutar da wani yaro ɗan shekara 12 da aka yi ƙoƙarin sace wa a cikin akwatin gawa da fararen kaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan
Mutanen sun yi ƙoƙarin fasa ƙwaurin yaron ne a cikin akwatin gawa yayin da asirin su ya tonu aka gane su.
Yayin da jami'an hukumar NIS suka ga motar basu amince da ita ba, sai suka tsayar da ita.
Rahoto ya bayyana cewa mutanen dake cikin motar sun tsere cikin daji yayin da jami'ai suka fara ƙoƙarin buɗe akwatin.
Hakan yasa jami'an NIS suka gano akwai rashin gaskiya a cikin akwatin gawan, kuma suka buɗe shi, inda suka ga yaron har ya fita daga hayyacinsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar tsaro ta NSCDC, Babawale Zaid Afolabi, yace jami'an NIS ne suka tare motar.
"Lokacin da jami'an NIS suka buɗe akwatin gawan, sun ga yaro ɗan shekara 12, wanda aka rufe shi da fareren kaya," inji shi.
An gwada lafiyar wanda aka kuɓutar
Babawale ya ƙara da cewa bayan sun gano ne sai suka sanar da hukumar NSCDC da sauran jami'an tsaron dake bakin iyaka.
KARANTA ANAN: Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno
Yace: "An yi wa yaron gwajin lafiya kuma an same shi cikik ƙoshin lafiya, yayin da binciken mu ya gano cewa yaron ɗan wani ƙauye ne a jamhuriyar Benin."
"A halin yanzun, an miƙa yaron ga jami'an yan sanda na jamhuriyar Benin domin cigaba da bincike har a miƙa shi ga iyalansa."
A wani labarin kuma Babbar Sallah: Wani Gwamnan Arewa Ya Bada Umarnin Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashi Kafin Sallah
Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya umarci ma'akatar kuɗin jihar ta biya ma'aikata albashin su kafin ranar salla.
Gwamnan ya kuma bada umarnin tura wa ma'aikata kuɗaɗen su kai tsaye maimakon bin ta hannun bankuna.
Asali: Legit.ng