Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan
- Yan bindiga sun sake kai hari garin Igangan da daren ranar Jumu'a, inda suka hallaka mutane da dama
- Rahoto ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka kashe a harin harda wani kwamandan jami'an tsaron Amotekun
- Jami'an sa kai da mafarauta sun samu nasarar korar yan bindigan, waɗanda ake zargin fulani makiyaya ne
Wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun sake kai hari Igangan, ƙaramar hukumar Ibarapa ta arewa, jihar Oyo, da daren ranar Jumu'a, inda duka kashe mutum huɗu, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno
Sai dai jami'an tsaron sa kai na yankin sun samu nasarar fatattakar maharan kafin su yi mummunar ɓanna.
Kwamandan jami'an tsaron Amotekun a ƙaramar hukumar Ibarapa, wanda aka bayyana sunansa da Muri, ya na daga cikin waɗanda suka rasa ransu.
Yan bindiga da kayan sojoji da na kwastam
Rahoton punch, ya nuna cewa maharan sun kai hari garin ne a cikin motar Hilux guda biyu, motar bus mai ɗaukar mutum 18, da kuma Toyota Sienna, suna sanye da kayan sojoji da kwastam.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun shigo garin da ɗumbin yawa amma ba zai iya faɗin adadinsu ba.
Wani sananne a garin Igangan, Oladiran Oladokun, ya tabbatar da harin, yace wannan farmakin wani ƙoƙarine na mamaye jihar amma jami'an tsaron sa kai na yankin suka daƙile shi.
Oladukon yace maharan sun zo cikin kayan sojoji da kwastam domin su yaudari mutanen gari, daga baya su canza lamarin.
Ya kuma bayyana rashin jin daɗinsa bisa rashin tsaro a yankin duk da ƙalubalen kawo hari da ake fuskanta.
Sun kashe kwamandan Amotekun
Wani shugaba a yankin, wanda ya yi jawabi cikin yaƙini, ya bayyana cewa:
"Na samu rahoton cewa da misalin ƙarfe 8:00 na dare wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun kai hari Igangan, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi na tsawon minti 30."
"Wasu mutane sun ce jami'an kwastam ne saboda sun sanya kayan jami'an, amma jami'an tsaron sa kai da mafarauta sun fatattake su."
"Maharan sun bi ta ƙauyen Igboora suna harbi kan mai uwa da wabi, sun kashe wasu mutane a can ciki harda kwamandan jami'an tsaron Amotekun."
KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Wani Gwamnan Arewa Ya Bada Umarnin Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashi Kafin Sallah
Da aka tuntuɓi wani jami'in Amotekun, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa jami'ai sun maida martani cikin gaggawa inda maharan suka tsere, amma sun kashe wasu mutane.
A wani labarin kuma Layin Dogo: Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Ma'aikata 20,000 Aiki, Minista
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi , ya bayyana cewa za'a ɗauki mutum 20,000 da zasu yi aiki a tashoshin jirgin ƙasa dake layin Kaduna-Kano.
Ministan yace ma'aikatarsa zata cigaba da aiki ba dare ba rana domin cika umarnin shugaba Buhari na zamanantar da layin dogo.
Asali: Legit.ng