Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno
- Wani turmutsutsin karɓar abinci a sansanin yan gudun hijira dake Monguno ya hallaka mata masu juna biyu
- Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mata 10 ne suka mutu, waɗanda mafi yawansu masu juna biyu ne ko shayarwa
- Ƙungiyar agaji ta Red Cross ce take raba wa yan gudun hijiran abinci yayin da lamarin ya faru
Aƙalla mata 10 waɗanda mafi yawan su masu juna biyu ko masu shayarwa ne suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin karbar abinci a Monguno, jihar Borno, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Wani Gwamnan Arewa Ya Bada Umarnin Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashi Kafin Sallah
Rahotanni sun bayyana cewa matan sun rasa rayukansu ne a turmutsutsin karɓar abincin da zasu ci a sansanin yan gudun hijira.
Wannan lamarin ya faru ne yayin da wata ƙungiya ta kai musu agajin abinci a sansanin yan gudun hijira dake Mungonu.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross, wanda ta raba abincin, ta bayyana rashin jik daɗin ta da faruwar lamarin.
Ƙungiyar ta yi gaggawar nemo kayan agaji domin taimakawa waɗanda suka ji raunuka yayin wannan turmushin.
An harba hayaƙi mai sa hawaye
Wata majiya ta bayyana cewa jami'an yan sanda ne suka harba hayaƙi mai sa ƙwalla domin tarwatsa taron.
"Mutane sun firgita, inda suka fara guje-guje bayan an harba hayaƙi mai sa ƙwalla domin tarwatsa taron." inji majiyar.
KARANTA ANAN: Layin Dogo: Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Ma'aikata 20,000 Aiki, Minista
Legit.ng hausa ta gano cewa aƙwai aƙalla yan gudun hijira 100,000 a sansanin dake Monguno, kuma dukkan su rikicin Boko Haram ne ya raba su da gidajensu.
A wani labarin kuma Rundunar Sojin Sama Ta Faɗi Ranar da Jiragen Yaki 'Super Tukano' Guda 6 Zasu Iso Daga Amurka
Rundunar sojin sama NAF ta tabbatar da cewa jiragen yaƙin super tucano guda shida sun baro Amurka.
A wani jawabi da kakakin NAF ya fitar, yace jiragen zasu biyo ta wasu ƙasashe biyar kafin isowar su.
Asali: Legit.ng