Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

- 'Yan bindiga sun hallaka wasu adadi na masu bautar da suka sace jiya Lahadi a Manini Tasha dake Chikun

- An ruwaito cewa, an sace mutanen da ba a san adadinsu ba, inda aka hallaka wani likita nan take

- Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an kashe mutanen, sannan ba ta san adadin da ke hannun 'yan bindigan ba

A harin da 'Yan bindiga suka kai Cocin Haske Baptist da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane takwas yayin da suka sace wasu masu bauta da yawa.

Sai dai, ba a tantance adadin wadanda aka sace ba, sun kuma samu raunuka daban-daban tare da wani likita, Zakariah Dogo Yaro na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin lamarin.

KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata

Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna
Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Cocin, wanda ke kauyen Manini Tasha, Kuriga Ward na karamar hukumar ta Chikun, maharan dauke da muggan makamai sun kai masa hari da misalin karfe 9 na safiyar Lahadi.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan Talabijin na Channels.

Wani memban cocin ya shaida wa wakilin gidan talabijin na Channels cewa da isowar ’yan bindigan suka kewaye cocin suka fara harbi ba ji ba gani kan masu bautar wadanda suka yi ta neman tsira a wurare daban-daban.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

A wani labarin, Har ila yau, ‘yan bindiga sun far wa masu bautar addinin kirista a cocin da ke kauyen Manini Tasha a karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna, a safiyar Lahadi.

An kashe mutum guda, wanda aka bayyana a matsayin likita, yayin da maharan suka sace wasu masu bautar da dama.

Wani ganau, wanda da kyar ya tsere daga abin da ya faru a Cocin na Haske Baptist da ke kauyen Manini, Mista Yakubu Bala, ya shaida wa Leadership cewa ’yan bindigan da ke dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin cocin inda suka yi wa masu ibadan dirar mikiya da misalin karfe 9 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel