Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati

Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati

- Kungiyar IPOB ta yi Allah wadai da kashe mata mambobi da kwamandan ESN da aka yi jiya

- Kungiyar ta zargi gwamna Uzodinma da hannu dumu-dumu cikin kashe mambobin na IPOB

- Kungiyar ta kuma bayyana cewa, gwamnan ya shirya don karbar martani nan ba da dadewa ba

Kungiyar 'Yan Asalin Biyafara (IPOB) ta yi Allah wadai da kisan mambobinta a jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Sojojin Najeriya sun ce jami'an tsaro sun kai samame a hedikwatar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) da ke jihar a ranar Asabar.

Mataimakin kwamandan kungiyar, wanda aka bayyana a matsayin kwamanda Ikonson da wasu mambobi shida sun mutu a yayin samamen.

Da yake mayar da martani a wata sanarwa, Emma da aka fi sani powerful, kakakin IPOB, ya yi Allah wadai da harin, ya kara da cewa kisan mambobinta "na da matukar zafi".

Ya ce Hope Uzodinma, gwamnan jihar, da duk wadanda ke da alhakin harin, za su biya sakamakon kisan.

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta haramta sayar da man fetur a wasu yankuna saboda 'yan bindiga

Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati
Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati Hoto: 3.bp.blogspot.com
Asali: UGC

“Mu danginmu na 'yan asalin Biyafara (IPOB) na duniya baki daya karkashin jagorancin babban jagoranmu Mazi Nnamdi Kanu, muna Allah wadai da harin bazata da aka kaiwa wasu mambobin kungiyar IPOB da jami’ai na ESN," inji shi.

“Kashe jaruman 'yan Biyafara marasa laifi da ke kare al’ummarmu da garuruwanmu daga Fulani ‘yan ta’adda makiyaya wadanda ke shiga irinta masu kiwon shanu, haka siddan ya mana da matukar zafi.

“Shugaban Kotun Koli na Jihar Imo Hope Uzodinma da duk wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aika za su biya sakamako da yawa.

"Hope Uzodinma da matsoratan jami'an tsaro na Najeriya wadanda ba za su iya fuskantar Fulani 'yan ta'adda ba sai dai kawai su nuna karfi idan suka ga masu fafutukar kafa kasar Biyafara.

"Saboda kisan Ikonso, Kwamandan ESN haka siddan, Uzodima ya tado da rikici! Ya kamata ya shirya don karbar martani.”

Kungiyar ta zargi Uzodinma da kashe Ikonso da mambobin kungiyar ta ESN saboda kin shiga Ebube Agu, kungiyar tsaro da gwamnonin kudu maso gabas suka kirkira.

"Don haka, saboda kin amincewarsu da cin amanar fafutukar neman kafa kasar Biyafara da Jagoranmu Mazi Nnamdi Kanu, gwamnan da ba shi da wata fata ya tattara jami'an tsaro na hadin gwiwa don kai musu hari a yau," in ji shi.

“Sun yiwa Ikonso kwanton bauna ne kawai amma mun musu alkawarin martani kan wannan hari na tsoro da suka yi!

"Hope Uzodinma kamar yadda ka ga gawar Ikonso a hannun Fulani 'yan a cikin 'yan sanda da sojojin Najeriya, haka zai zama sakamakon ka wata rana."

KU KARANTA: Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro, Amma Babu Kudi, Minista

A wani labarin, Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya. '

Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021.

Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.