El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani

El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani

- Gwamnan jihar Kaduna ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai Cocin Chikun

- Ya siffanta harin a matsayin mugunta tsarogoranta kan mutane marasa laifi masu zama lafiya

- Ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu da kuma Cocin baki daya

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan Cocin Haske Baptist da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

‘Yan bindiga sun mamaye cocin a safiyar ranar Lahadi, inda suka kashe wasu masu bauta tare da yin awon gaba da wasu.

Shi ma wani mazaunin yankin Shehu Manika, an ce an ji masa rauni a yayin lamarin, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Kano Ta Lalata Jabun Kayayyakin Abinci da Ake Sayarwa Al'umma na Kimanin N1bn

El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani
El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani Hoto: icirnigeria.org
Asali: UGC

Yayin da yake Allah wadai da harin a cikin wata sanarwa daga Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida, gwamnan ya ce irin wannan mamaye cocin mugunta ne tsagoronsa kuma mummunan yanayi.

"Gwamna Nasir El-Rufai ya fito karara ya yi tir da harin da aka kai wa cocin a karamar hukumar Chikun a matsayin wani abin firgitarwa na lalalatattun mutane da suka yi nesa da mutane," in ji sanarwar.

“Gwamnan ya kara da cewa afkawa masu bautar marasa laifi da ke amfani da hakkinsu na dabi’a kuma halastacce don taruwa a cikin sujada, yana wakiltar mafi munin nau'in mugunta.

"Gwamnan ya aika da ta'aziya zuwa ga iyalan mamatan da kuma Cocin Haske Baptist."

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

A wani labarin, A harin da 'Yan bindiga suka kai Cocin Haske Baptist da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane takwas yayin da suka sace wasu masu bauta da yawa.

Sai dai, ba a tantance adadin wadanda aka sace ba, sun kuma samu raunuka daban-daban tare da wani likita, Zakariah Dogo Yaro na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin lamarin.

Cocin, wanda ke kauyen Manini Tasha, Kuriga Ward na karamar hukumar ta Chikun, maharan dauke da muggan makamai sun kai masa hari da misalin karfe 9 na safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel