Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya

Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya

- Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa, Najeriya za ta ci gaba nan gaba kadan

- Ya yi bayanin cewa, akwai alkawarin ubangiji tattare da Najeriya na zaman lafiya da arziki

- Ya kuma bayyana karara idan matsalolin da sassan kasar ta Najeriya ke fuskanta a yanzu

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya ce "akwai alkawarin Allah" ga Najeriya kuma kasar za ta zama "gidan zaman lafiya, tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a wannan nahiya da ma ta gaba da ita."

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jawabi a wajen babban taron shekara-shekara karo na 108 na Babban Taron Baptist na Najeriya a Jihar Ogun, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa Najeriya "za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21," a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu akai.

KU KARANTA: El-Rufa'i Ya Yi Allah Wadai da Harin 'Yan Bindiga a Coci, Ya Mai da Martani

Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya
Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, ba mai iya ja da lamarin Allah ko wane ne shi inda yake cewa: “Ina da cikakken yakinin cewa babu wani, babu wata kungiya, ko wata akida, da za ta iya karya alkawarin Allah don cigaban Najeriya."

Sai dai, ya lura cewa "a yau gizagizai sun lullube, alkawarin kamar ba zai yiwu ya cika ba, kamar yadda ya kasance ga 'ya'yan Isra'ila bayan barinsu Misira kan hanyar su zuwa kasar da aka alkawarta musu."

Kalaman na Mataimakin Shugaban na zuwa ne yayin da kasar ke ci gaba da fama da kalubalen tsaro da dama.

Kasar na fuskantar matsaloli kamar tayar da kayar baya a Arewa-maso-Gabas, 'yan ta'adda a yankin Arewa-maso-Yamma, da tayar da zaune tsaye a Kudu-maso-Gabas da rikicin Fulani-makiyaya a duk yankin na Tsakiyar Arewaci da kuma jihohin Kudu maso Yamma da dama.

KU KARANTA: Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

A wani labarin daban, Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa gidan Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga sun mamaye gidan Uzodinma da ke Omuma a karamar hukumar Oru inda suka kona wani bangare na ginin tare da kashe wasu jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki.

Jam’iyyar ta APC ta kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kaiwa jami’an ‘yan sanda da kuma cibiyoyinsu a Abia, Imo, Ebonyi, Anambra da Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel