APC Ta Fusata da Hare-Hare a Imo, Ta Ce Ba Za Ta Bari Imo Ta Zama Filin Kashe-Kashe Ba

APC Ta Fusata da Hare-Hare a Imo, Ta Ce Ba Za Ta Bari Imo Ta Zama Filin Kashe-Kashe Ba

- Jam'iyyar APC ta bayyana jimaminta ga kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar Imo

- Ta kuma jajantawa Gwamna Uzodinma na jihar bisa harin da aka kai gidansa a jihar ta Imo

- Hakazalika jam'iyyar ta ce ba za ta zura ido tana kallo a lalata jihar ta zama filin kashe-kashe ba

Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa gidan Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga sun mamaye gidan Uzodinma da ke Omuma a karamar hukumar Oru inda suka kona wani bangare na ginin tare da kashe wasu jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki.

Jam’iyyar ta APC ta kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kaiwa jami’an ‘yan sanda da kuma cibiyoyinsu a Abia, Imo, Ebonyi, Anambra da Ribas.

A wata sanarwa daga John Akpanudoedehe, jigo a jam'iyyar APC ya bayyana harin da aka kai gidan Uzodinma a matsayin "hari ne ga dimokiradiyya da kuma kafaffiyar hukuma wacce ke aiki don biyan bukatun mutanen Imo".

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

Jam'iyyar APC: Ba za mu taba bari jihar Imo ta zama dandamalin yaki ba
Jam'iyyar APC: Ba za mu taba bari jihar Imo ta zama dandamalin yaki ba Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Jam’iyyar ta ce “Jam’iyyar APC ta sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a jihar Imo wadanda suka kai ga harin bazata da aka kaiwa gidan gwamnan jihar, Sen. Hope Uzodimma a ranar Asabar.

“Mun tsaya tare da rundunar 'yan sanda ta Najeriya da kuma iyalan wadanda abin ya shafa a wannan mawuyacin lokaci yayin da muke jimamin mutuwar jami’an tsaro da ba su da laifi kuma masu kwazo dake gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyi.

“Jam’iyyar da kuma jami’an tsaronmu ba za su zura ido suna kallo ba yayin da wasu mutane da masu son rai ke kokarin mayar da jihar Imo filin kashe-kashe.

"Muna kira ga mutanen kirki na jihar Imo da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na bin doka ba tare da tsoro ba kuma su yi barranta da wadannan makiya jihar.”

Jam’iyyar ta nemi hukumomin tsaro da su zakulo wadanda ke kai hare-haren da wadanda ke daukar nauyinsu kuma su tabbatar da an ladabtar dasu don dawo da martaba ga 'yan kasa.

KU KARANTA: Karin Bayani: An Hallaka Mutane 8 Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Coci a Kaduna

A wani labarin, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan Cocin Haske Baptist da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

‘Yan bindiga sun mamaye cocin a safiyar ranar Lahadi, inda suka kashe wasu masu bauta tare da yin awon gaba da wasu.

Shi ma wani mazaunin yankin Shehu Manika, an ce an ji masa rauni a yayin lamarin, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.