Gwamna matawalle ya tsige sarkin Maru da wani saboda zargin tallafawa ta'addanci

Gwamna matawalle ya tsige sarkin Maru da wani saboda zargin tallafawa ta'addanci

- Gwamna Matawalle ya sanya matakan hukunta jami’an da ake zargi da tallafawa ‘yan bindiga

- Jihar ta Zamfara ta sha samun hare-hare da dama daga wasu mahara 'yan bindiga

- Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa ‘yan siyasa na marawa kungiyoyin bindiga baya

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tsige mai martaba Sarkin Maru, Abubakar Chika, bisa zargin ba da goyon baya ga 'yan bindiga.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gwamnan ya kuma tsige shugaban gundumar Kanoma, Lawal Ahmed kan wannan laifin da ake zarginsu da shi.

Kungiyar koli ta arewa, ACF ta jinjinawa gwamnan game da irin matakin da ya dauka kan magoya bayan 'yan bindiga.

KU KARANTA: Sufeto-Janar na 'yan sanda Adamu: Zan iya zama daram a ofis har zuwa 2023 ko 2024

Gwamna matawalle ya tsige sarkin Maru da wani saboda zargin tallafawa ta'addanci
Gwamna matawalle ya tsige sarkin Maru da wani saboda zargin tallafawa ta'addanci Hoto: The Guardian
Source: Twitter

Jaridar This Day ta ruwaito kakakin kungiyar kolin, Emmanuel Yawe, ya ce matakin da gwamnan ya dauka ya dace.

A cewar Yawe, an dakatar da sarkin da hakimin tun a watan Yunin 2020 yayin da ake kan bincike.

Ya ce an same su da laifin ne bayan korafe-korafen da talakawansu suka yi na cewa suna hada kai da ’yan bindiga da masu satar mutane.

Kungiyar ta ce:

"Mu mutanen ACF muna taya gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bello Mutawale murnar daukar wadannan kwararan matakan."
“Allah Madaukaki wanda ba ya barci zai kiyaye shi. Babu abin da zai same shi. ''

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ‘yan Najeriya za su yi mamaki idan aka ba su labarin wadanda ke da hannu wajen sace 'yan mata ’yan makaranta sama da 300 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Matawalle ya yi wannan bayanin ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da Sarakuna 17 a jihar suka kai masa ziyarar jajantawa kan sace daliban.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel