Matawalle: Zaku sha mamaki idan na tona asirin masu hannu a sace daliban Jangebe

Matawalle: Zaku sha mamaki idan na tona asirin masu hannu a sace daliban Jangebe

- Bello Matawalle ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya game da sace 'yan makarantar GGSS da aka yi a jihar Zamfara

- Gwamnan ya bayyana dalilin da yasa yake ganin akwai makircin yiwa gwamnatin sa zagon kasa

- Matawalle ya kasance yana tallata manufar kulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga a baya

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ‘yan Najeriya za su yi mamaki idan aka ba su labarin wadanda ke da hannu wajen sace 'yan mata ’yan makaranta sama da 300 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Matawalle ya yi wannan bayanin ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da Sarakuna 17 a jihar suka kai masa ziyarar jajantawa kan sace daliban.

Gwamnan ya ce wadanda suke da hannu a satar 'yan makarantar da aka yi kwanan nan a cikin jihar suna kokarin yin zagon kasa ga ci gaban da ya kawo baya na samar da zaman lafiya a jihar.

KU KARANTA: Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO

Zamfara: Matawalle ya tona asirin masu hannu wajen sace daliban Jangebe
Zamfara: Matawalle ya tona asirin masu hannu wajen sace daliban Jangebe Hoto: @bellomatawalle1
Asali: UGC

Ya ce: ‘’Yayin da muke jiran isowar daliban da aka sako na GSSS Jangebe a gidan gwamnati a yau, ina so in sanar da ku cewa akwai boyayyun abubuwa da yawa dangane da sace wadannan daliban.”

"Mutane da yawa za su yi mamakin jin wadannan mutane dake da hannu a sace wadannan yara marasa galihu."

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta ce daliban da aka sace na Sakandaren Gwamnati da ke Jangebe, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su.

Yusuf Idris, mai taimaka wa gwamna Bello Matawalle a fannin kafafen yada labarai, ya ba da bayani a ranar Lahadi, 28 ga Fabrairu, yayin da rahotanni ke yawo cewa an sako ‘yan matan.

Idris wanda yayi magana ga manema labarai da misalin karfe 3 na rana jiya Lahadi ya sanar da cewa ba a sako daliban da aka sacen ba, yana mai cewa a yanzu haka ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da yaran cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: Sunday Igboho: Sai na kafa Jamhuriyar Oduduwa, kuma zan kashe Yarbawa masu hana ni kafin 2023

A wani labarin, A baya mun kawo muku rahoton cewa, an saki daliban makaranta sakandaren 'yan mata dake Jangebe a jihar Zamfara.

Sai dai,a yanzu mun samu rahoto daga tushe mai karfi cewa ba a sake su ba tukuna.

Daliban da aka sace daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su, in ji gwamnatin jihar.

Yusuf Idris, mai taimaka wa Gwamna Bello Matawalle a harkar yada labarai, ya shaida wa PremiumTimes da misalin karfe 3 na rana, a ranar Lahadi cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an sake su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel