Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya

Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya

- Gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana cewa, za ta kirkiri filayen kiwo ga makiyaya a jihar ta Ekiti

- Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, ba zata lamunci kisan manoma da wasu makiyaya ke yi ba

- Hakazalika, gwamnatin jihar ta bayyana biyayyatar ga umarnin shugaba Buhari na hukunta masu rike da muggan makamai

A wani bangare na hanyoyin kawo karshen rikice-rikicen makiyaya da manoma, gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana cewa za ta sanya hannu cikin shirin sauya fasalin kiwo na Gwamnatin Tarayya ta hanyar kirkirar wuraren kiwo a cikin jihar.

Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki uku bayan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe wasu manoma biyu a Isaba-Ekiti, da ke karamar hukumar Ikole, ta jihar, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa, a ranar Litinin, ta hannun Kwamishinan yada labarai, Akin Omole, gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta yarda da kisan manoma da mazauna jihar ba ta hanyar wasu makiyaya masu aikata laifuffuka da ke shiga cikin gonaki.

A cewarsa, gwamnan jihar, Dakta Kayode Fayemi, ya bai wa ‘yan sanda da kuma Amotekun cikin awanni 24 da su kakkabe dazuzzukan Karamar Hukumar tare da amintar da ita daga sake kai hari.

KU KARANTA: Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta

Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya
Gwamnatin jihar Ekiti za ta kirkiri kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Gwamnatin ta sake nanata kudurin kwanan nan na taron zaman lafiya tsakanin gwamnoni da shugabannin kungiyar Miyetti Allah a Akure, babban birnin jihar Ondo game da dokar hana kiwo na kananan yara, a cikin dare da ma kiwo a fili a jihar.

Omole ya ce: “A bayyane yake cewa yankin Ikole/Oye na jihar na iya fuskantar kutse daga masu son aikata laifuka wadanda ke son yin amfani da damar yanayin dajin don aikata ta’addancin da bai dace ba a kan al’ummomin manoma a yankin. Ba za mu bari wannan ya faru ba.

“Muna sake nanata cewa bisa hadin gwiwar taron zaman lafiya na Akure da aka yi a kwanan nan da kuma yarjejeniyar hadin gwiwa da aka fitar tsakanin Gwamnonin Kudu maso Yamma da Miyetti Allah, har yanzu ana hana kiwo a fili/dare da kananan yara a Jihar Ekiti.

"Hakanan jihar tana yin wasu tsare-tsare na daban domin kiwo/kiwo a karkashin shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a cikin jihar.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa jami'an tsaro a jihar za su aiwatar da sabuwar dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar kan wadanda ke amfani da muggan makamai.

"Hakazalika, daidai da umarnin da Shugaban Kasa ya bayar na kwanan nan, duk wanda ke dauke da mugun makami da aka samu a dazukan Ekiti za a dauke shi a matsayin mai laifi mai hadari kuma za a mika shi ga jami'an tsaro domin a hukuntashi yadda ya kamata,"

Gwamnatin ta shawarci mazauna Isaba-Ekiti da su tallafawa jami’an tsaro da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen cafke masu laifin, sannan ta kara da cewa, “ya ​​kamata su ci gaba da gudanar da halattatun harkokinsu; mun dukufa kan kare rayuka da dukiyoyi.”

KU KARANTA: Babu wanda zai tsira sai kowa yayi rigakafin Korona, in ji Boss Mustapha

A wani labarin daban, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba ya nanata cewa jihar ba za ta bayar da filaye kyauta don kiwo ba, yana mai cewa kiwo kasuwanci ne na kashin kai, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter yayin da yake karin bayani kan wani bayani da ya gabatar a baya game da shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a yayin taron tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel