Kada ku tausayawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda

Kada ku tausayawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda

- IGP na 'yan sandan Najeriya ya umarci 'yan sanda kan kausasawa 'yan ta'adda a kasar

- Ya kuma bayyana cewa, su zauna lafiya da masu bin doka da oda a duk inda suke a kasar

- Ya kuma tabbatar da samar da isassun kayan aiki don yakar 'yan ta'adda a yankin arewa

Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci jami’an rundunar‘ yan sanda ta Najeriya da su jajirce tare da nuna rashin tausayi akan “masu aikata laifuka”, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar, da ke Abuja, yayin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro, wanda aka sanya wa suna “Operation Puff Adder II”, don karfafa yakin da ake yi da ‘yan fashi, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kasar.

Yayin da yake baiwa 'yan sanda tabbacin samar da wadatattun kayan aiki, ya bukace su da su kasance masu zama tare da masu bin doka da oda, sannan ya kara da cewa sabon aikin na musamman zai kasance karkashin jagorancin leken asiri da kuma jagorancin al'umma.

KU KARANTA: Okonjo-Iweala za ta zama mace kuma 'yar Afrika ta farko a matsayin DG na WTO a yau

Kada ku tausawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda
Kada ku tausawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda Hoto: The Punch News
Source: Twitter

Ya ce za a aiwatar da wannan sabon aikin ne tare da hadin gwiwar Dakarun Soji, Kungiyar Leken Asiri da sauran hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa, “Wannan kaddamar da tutar shi ne bangare na farko na aikin da aka yi niyya da maido da zaman lafiya da tsaro a shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da yankin tsakiyar kasar.

“Aikin an yi shi ne domin fatattakar 'yan fashi daga wuraren da suke gudanar da ayyukansu a yanzu tare da hana su damar sake haduwa a wasu sassan kasar.

“Hakan kuma zai tabbatar da cewa an gurfanar da duk 'yan fashin da aka kama tare da wadanda suka hada kai da su. Nan gaba, ana sa ran za a maimaita aikin a duk sauran jihohin Tarayyar don magance matsalolin tsaro da ke cikin wadannan Jihohin.”

KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

A wani labarin, Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunoni hudu na 'yan sandan kwantar da tarzoma don magance rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan jihar Oyo, The Punch ta ruwaito.

Shiga tsakani da rundunar kwantar da tarzomar sun hada da jami'an Ofishin Leken Asirin na kasa da kuma helikopta mai sa-ido guda daya daga sashen jigilar 'yan sanda.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel