Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta

Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta

- Tsohuwar matar Jeff Bezos ta auri wani malamin makaranta mai zaman kanta bayan rabuwarta da Jeff Bezos

- Matar ta rabu da Jeff Bezos a shekarar 2019 kuma a yanzu ta auri malamin makaranra da take so

- Jeff Bezos bai nuna rashin jin dadi ba, karshe ma ya musu fatan alheri da addu'ar zaman lafiya

MacKenzie Scott, tsohuwar matar wanda ya kafa kamfanin Amazon Jeff Bezos, ta auri wani malamin da ke koyarwa a makaranta mai zaman kanta inda ‘ya’yanta ke karatu, The Nation ta ruwaito.

Scott, wanda a da aka fi sani da MacKenzie Bezos kuma mai kimar kimanin dala biliyan 53, ta saki mijinta mai kamfanin Amazon a shekarar 2019 bayan shekaru 25 da aure.

Sabon mijin mai shekaru 50 shine Dan Jewett, malamin kimiyya ne a makarantar Seattle Lakeside mai zaman kanta inda yaran da take tare da Bezos suke karantu.

Ba a bayyana ba tukuna lokacin da Scott da Jewett suka yi aure ko tsawon lokacin da suka kasance tare.

KU KARANTA: Yanzun nan: 'Yan bindiga sun sake sace mutum 19 a wani kauyen jihar Neja

Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta
Tsohuwar Matar Jeff Bezos: Ta rabu da mai kudin duniya ta auri malamin makaranta Hoto: The Nation
Asali: UGC

Bezos, wanda ke da yara hudu da tsohuwar matar tasa, ya fada a cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawun kamfanin na Amazon cewa: "Dan babban mutum ne, kuma na yi farin ciki ga su biyun," kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Ma'auratan sun fara ambata aurensu a bainar jama'a a ranar Asabar a wani rubutu da aka yi a kan alkawarin aurensu, a wani shafin da attajirai da fitattu suka sha alwashin sadaukar da dukiyoyinsu ga wasu.

Scott, wacce marubuciya ce kuma mai son taimakon jama'a, ta kuma canza shafinta na rayuwar Amazon inda ta ce tana zaune a Seattle tare da 'ya'yanta hudu da mijinta Dan.

Makarantar mai zaman kanta inda Jewett ke koyarwa da ‘ya‘ yan matar sa suna aji 5 zuwa 12 kuma tana biyan $38,000 a duk shekara.

Shahararrun tsofaffin dalibai na makarantar mai zaman kansu sun hada da Bill Gates.

A cikin wani sako a shafin, Jewett ya ce yana hada hannu da matar sa na sadaukar da dimbin dukiyar kudi don yi wa wasu hidima.

Tun rabuwarta da Bezos a cikin 2019, Scott - wanda ta taimaka wajen ƙirƙirar Amazon - ta riga ta sadaukar da wani bangare na dukiyarta.

Ta ba da kusan dala biliyan 6 a bara kadai.

KU KARANTA: Babu wanda zai tsira sai kowa yayi rigakafin Korona, in ji Boss Mustapha

A cikin wani matsakaiciyar sanarwa a cikin watan Disamba, Scott ta bayyana cewa ta bayar da dala biliyan 4.1 a cikin watanni hudu da suka gabata ga daruruwan kungiyoyi a wani yunkuri na taimakawa wadanda cutar Korona ta shafa.

Ta taba bayar da gudummawar dala biliyan 1.68 ga kungiyoyi masu zaman kansu 116, jami'o'i, kungiyoyin ci gaban al'umma, da kungiyoyin shari'a a watan Yulin shekarar 2020.

A wani labarin daban, Babban jami'in kamfanin Tesla, Elon Musk, ya sauka daga matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a duniya; shugaban kamfanin Amazon ya karbe matsayin, Legit.ng ta gano.

A cewar Bloomberg, hannun jarin Tesla ya fadi kasa da kashi 8.6% a ranar Litinin, 22 ga Fabrairu, tare da rasa dala biliyan 15.2 (N5,795,000,000,000) daga dukiyar Musk.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.