Amurka ta sayarwa Najeriya jiragen yaki guda 12 kirar A-29 Super Tucano don yakar 'yan ta'adda

Amurka ta sayarwa Najeriya jiragen yaki guda 12 kirar A-29 Super Tucano don yakar 'yan ta'adda

- Kasar Amurka ta sayarwa Najeriya jirage domin yakar 'yan ta'adda a yankunan kasar

- Kasar Amurka ta kuma bayyana ci gaba da hada kai da Najeriya wajen yakar 'yan ta'adda

- Hakazalika Najeriya na tsammanin isowar jiragen nan ba da dadewa ba cikin wannan shekarar

Kwamandan Sojin Amurka a yankin Afirka, Janar Stephen Townsend ya ce za a kawo jiragen nan guda goma sha biyu na yaki kirar A-29 Super Tucano da Najeriya ta saya daga Amurka a cikin wannan shekarar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Townsend ya bayyana hakan ne a wata sanarwa bayan ya kammala ziyarar kwanaki uku na Yammacin Afirka tare da tsayawa a Najeriya, ranar Juma'a.

“A matsayin kawaye na kud da kud, Amurka da Najeriya sun yi aiki don tabbatar da alakar hadin gwiwa ta ci gaba da bunkasa don kokari da kuma sadaukar da kai.

"Najeriya ta sayi jirgin yaki mai saukar ungulu guda 12 kirar A-29 Super Tucano, wanda za a kawo nan gaba a wannan shekarar," in ji shi.

KU KARANTA: Karin bayani: Ba a saki daliban makarantar Jangabe ba tukuna

Amurka ta sayarwa Najeriyajiragen yaki guda 12 kirar A-29 Super Tucano don yakar 'yan ta'adda
Amurka ta sayarwa Najeriyajiragen yaki guda 12 kirar A-29 Super Tucano don yakar 'yan ta'adda Hoto: The Defense Post
Asali: UGC

Ya ce Kwamitin Afirka na sojin Amurka zai yi iya kokarinsa don inganta ginshikin hadin gwiwar tsaro, ta yadda 'yan Najeriya za su more rayuwa mai aminci da suka cancanta.

Townsend ya gana da Shugaban Ma’aikatan Najeriyar, Ibrahim Gambari, da mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, inda suka tattauna kan al’amuran tsaro na yankin.

Kuma sun nuna godiyar rundunar game da taimakon da aka bayar yayin ayyukan ceton wadanda aka yi garkuwa da su a bara.

“Lokacin da muka nemi taimakon su, gwamnatin Najeriya ta amsa kiran. Manufarmu ta dawo da wadanda aka yi garkuwa da su a watan Oktoba ba zai yiwu ba tare da goyon bayansu ba.

“Nan da nan suka ba da taimako wanda ya taimaka wa sojojin Amurka don ceton rayuwar Ba’amurke. Wannan babban misali ne na hadin gwiwarmu da Najeriya ”, in ji sanarwar.

Mista Townsend ya kuma gana da manyan hafsoshin soja, ciki har da Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Leo Irabor, don tattaunawa kan ci gaba da hadin kai a yankin da kuma inganta tsaro a cikin teku da rage barazana ga kasar.

Najeriya babbar kawa ce ga kawar da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a duk fadin Tafkin Chadi.

"Shugabannin Najeriya sun fahimci mahimmancin tsarin hadin gwiwa don tabbatar da kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma da kuma hadin gwiwa a bangarorin da suka shafi moriyar juna," in ji Mista Townsend.

Hakanan a cikin sanarwar, Jakadiya Linda Thomas-Greenfield daga Ofishin Jakadancin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce Amurka ta yi Allah wadai da mummunan sace 'yan mata sama da 300 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati da ke Jangebe a Najeriya.

KU KARANTA: Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO

A wani labarin, Fitaccen dan gwagwarmayar nan na Yarbawa, Sunday Adeyemo, ya fara tsokano kafa Jamhuriyar Oduduwa, yana barazanar kawar da 'yan siyasar Yarbawa da zasu ki mara wa shirin nasa baya kafin 2023.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu kuma aka fassara, Mista Igboho yayin da yake zantawa da shugabannin Yarbawa da matasa, ya ja kunnen ‘yan siyasan kan rashin nuna damuwar su ga Jamhuriyar Oduduwa.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel