Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO

Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO

- Hukumar DSS ta shaidawa jama'a cewa ba dalilin kakkausar magana ne yasa aka kame Yakasai ba

- Sun bayyana batun kama shi ya zarce maganar da yayi na suka ga gwamnatin shugaba Buhari

- Hakazalika DSS tace wannan shine sanarwa kan cewa yana hannunsu kuma suna ci gaba da bincike

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce kame Malam Salihu Tanko-Yakassai, hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya biyo bayan batutuwan da suka wuce na bayyana ra'ayi a kafafen sada zumunta.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, Vanguard News ta ruwaito.

KU KARANTA: Sunday Igboho: Sai na kafa Jamhuriyar Oduduwa, kuma zan kashe Yarbawa masu hana ni kafin 2023

Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO
Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO Hoto: BBC
Asali: UGC

"Wannan shi ne tabbatar da cewa Salihu Tanko-Yakasai yana tare da DSS kuma ana bincikensa kan batutuwan da suka wuce na bayyana ra'ayi a kafafen sada zumunta kamar yadda wasu jama'a suka yi zargi bisa kuskure, "

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya kawo cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamna Ganduje ya kori mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai bisa zargin wasu maganganu da ya furta ba tare da taunasu ba.

Ya ce Tanko-Yakassai ya kasa bambance tsakanin ra'ayin mutum da matsayar hukuma kan al'amuran da suka shafi jama'a. Don haka, in ji shi, ba za a ba shi damar ci gaba da aiki a gwamnatin da bai yi imani da ita ba.

KU KARANTA: Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga

A wani labarin daban, Hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta tabbatar da cewa ita ta garkame Salihu Tanko-Yakasai tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ya biyo bayan sallamarsa da gwamnan Kanon yayi ranar Asabar.

A jawabin da kakakin hukumar DSS< Peter Afunanya ya saki da yammacin asabar, ya tabbatar da cewa lallai Tanko Yakassai na hannunsu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: