Sunday Igboho: Sai na kafa Jamhuriyar Oduduwa, kuma zan kashe Yarbawa masu hana ni kafin 2023
- Fitattacen dan gwagwarmayar Yarbawa ya gargadi danginsa kan neman zaben shkarar 2023
- Yayi alwashin cewa zai kashe su kafin zaben na 2023 matukar basu mara masa baya a manufarsa ba
- Ya bayyana manuarsa kai tsaye na son raba Yarbawa da gwamnatin Najeriya nan ba da dadewa ba
Fitaccen dan gwagwarmayar nan na Yarbawa, Sunday Adeyemo, ya fara tsokano kafa Jamhuriyar Oduduwa, yana barazanar kawar da 'yan siyasar Yarbawa da zasu ki mara wa shirin nasa baya kafin 2023.
A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu kuma aka fassara, Mista Igboho yayin da yake zantawa da shugabannin Yarbawa da matasa, ya ja kunnen ‘yan siyasan kan rashin nuna damuwar su ga Jamhuriyar Oduduwa.
A cewarsa, bai kamata 'yan siyasar Yarbawa su yi ihun neman shugabanci na 2023 a wannan lokacin ba, sai dai su kasance a sahun gaba na shirin ballewar da shi da sauran 'yan Kudu Maso Yamma ke goyon baya.
Lokacin da aka tuntube shi kan barazanar bidiyon Sunday Igboho, kakakin Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), Dokta Peter Afunanya ya shaida wa PRNigeria cewa hukumar leken asirin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin ka'idojin da doka ta ba ta.
KU KARANTA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana
Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce:
“Idan da ku (masu rike da mukaman siyasa a Yarbawa) duk ba wakilai ne marasa amfani ba, ya kamata ku shugabance mu a gwagwarmayar ballewar. Amma kun shagaltar da yakin neman zaben Shugaban kasa mai zuwa. Lallai kun cika mahaukata.
“Ya kamata ku sani cewa bai kamata ku nemi zabe zuwa ofishin Shugaban kasa ba, ya kamata ku yi la’akari da hayaniyar mu (Yarbawa) kuma ku jagorance mu a fafutukar ballewar.
“Ba zan ba ku damar yin kamfen ba saboda zan kashe ku duka (‘yan siyasar Yarbawa) kafin fara kamfen (a 2023), na rantse da Allah.
“Ba zan ba ku damar yin kamfen ba saboda za mu kashe ku duka (‘yan siyasar Yarbawa) kafin yakin neman zaben su. Na rantse da Allah. Ko dai su tafi wani wuri ko kuma mu harbe su da bindigogi daga baya.
“Ina kira gare ku dattawan Yarbawa, sarakunan gargajiya da ku jagorance mu zuwa yakin ballewar Jamhuriyar Oduduwa mai zaman kanta. Kada mu ji tsoro ...
“Za mu samu karin kudi saboda muna da danyen mai da teku (don dorewar tattalin arzikin Jamhuriyar Oduduwa). Za mu fi jin dadin sabuwar kasarmu.
“Idan kun goyi bayan shirinmu na ballewa, za mu sha wahala kasa da makonni biyu kawai sannan daga baya mu more arzikinmu.
"Me yasa ku (yan siyasa) masu son kai, kuke neman muyi muku yakin neman shugabancin Najeriya a 2023? Shin kunyi hauka ne? Ku je ku iyakance yakin neman zaben ga danginku. Idan kuka yi kamfen a cikin jama’a, zan yake ku."
“A watan Oktoban da ta gabata na yi kashedi ga wasu dattawanmu da shugabanninmu tun kafin masu zanga-zanga su kunyatar dasu da wulakanta su… Wannan shi ne farkon zamu fito nan ba da jimawa ba.
Ina kira ga mabiyana da su je su shirya tsubbace-tsubbacensu don yanke shawara game da Jamhuriyar Oduduwa. Dole ne mu raba kasar nan… Ba mu son zama (a Najeriya) kuma.
“Sarakunan gargajiyanmu matsorata ne kuma suna biyayya ga umarni daga kansilolin yankin. Kwanan nan na samu labarin cewa wani sarkin Yarbawa ya yi wa wata mata mai fafutukar ballewar yankinda ke zaune a Jamus barazanar kada ta dawo kasar.
“Yanzu haka ina kira ga matar da ta zo kuma zan yi farin cikin karban ta da kuma kare ta a filin jirgin sama.
“Watakila a wannan ranar, za mu iya canza sunan Filin jirgin saman Murtala na (Lagos) zuwa Filin jirgin sama na Awolowo.
“Wasu daga cikin dattawanmu marasa amfani sun sanya sunan Filin Jirgin samanmu Murtala Airport maimakon sanya masa suna da kansu maimakon sunan Fulani. Dattawan Yarbawa da ke bayan sanya sunan filin jirgin saman gungun mahaukata ne.
“Yakin gaske wanda zai kawo karshen komai zai faru ne a ranar da zan tarbi mace mai fafutukar ballewar (Yarbawa) a filin jirgin sama. Idan sun isa kuskura su taba ni," ya kammala.
KU KARANTA: Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne
A wani labarin, Shararren marubuci Farfesa Wole Soyinka, a ranar Asabar ya ce daga yanzu, duk jihar da ake satar yara ya kamata ta rufe don nuna rashin amincewa da ta'addancin, The Punch ta ruwaito.
Soyinka ya kuma shawarci sauran jihohin da ke makwabtaka, a matsayin hadin kai, su ma su shiga zanga-zangar tare da rufe jihohinsu.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng