Karin bayani: Ba a saki daliban makarantar Jangabe ba tukuna

Karin bayani: Ba a saki daliban makarantar Jangabe ba tukuna

- Gwamnatimn jihar Zamfara ta tabbatar da cewa, zuwa yanzu ba a saki daliban GGSS Jangebe ba

- Gwamnatin ta yi kira ga watsi da duk wasu labarai da ke cewa an saki daliban a yau din nan

- Gwamnati ta roki iyaye da su ci gaba da adduar Allah ya bada nasarar kubutar da daliban

A baya mun kawo muku rahoton cewa, an saki daliban makaranta sakandaren 'yan mata dake Jangebe a jihar Zamfara. Sai dai,a yanzu mun samu rahoto daga tushe mai karfi cewa ba a sake su ba tukuna.

Daliban da aka sace daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su, in ji gwamnatin jihar.

Yusuf Idris, mai taimaka wa Gwamna Bello Matawalle a harkar yada labarai, ya shaida wa PremiumTimes da misalin karfe 3 na rana, a ranar Lahadi cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an sake su.

Ya yi wannan bayani ne biyo bayan rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar cewa an sake 'yan matan.

Mista Idris ya ce gwamnan ya kammala ganawa da sarakunan gargajiya a jihar ne a gidan gwamnati da ke Gusau don ganin an dawo da daliban lafiya.

KU KARANTA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

Karin bayani: Ba a saki daliban makarantar Jangabe ba tukuna
Karin bayani: Ba a saki daliban makarantar Jangabe ba tukuna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Abutu Yaro, shi ma ya ce har yanzu ba a sako 'yan matan ba.

“Ina so in ja hankalin mutanen kirki na jihar Zamfara, ya kamata su yi watsi da duk wani labarin karya game da sakin daliban GGSS Jangebe da wani kamganin jarida keyi. Ba gaskiya bane.

"Amma, Alhamdulillah, gwamnatin jiha da jami'an tsaro suna iya bakin kokarinsu,” ya ce a cikin wani gajeren sakon da ya gabatar ga wakilin Premium Times.

Mai magana da yawun gwamnan, Mista Idris, ya kuma bukaci jama'a da su yi watsi da rahotannin da kafafen yada labarai ke yada cewa an saki daliban, yana mai kira ga iyayen yara da mazauna jihar da su yi addu’ar Allah ya dawo da daliban lafiya.

Jami'in ya ce "Gwamnatin jihar ta himmatu domin dawo da daliban lafiya ko ba jima ko ba dade, ya kamata mu yi hakuri," in ji jami'in.

KU KARANTA: Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne

A wani labarin, Shararren marubuci Farfesa Wole Soyinka, a ranar Asabar ya ce daga yanzu, duk jihar da ake satar yara ya kamata ta rufe don nuna rashin amincewa da ta'addancin, The Punch ta ruwaito.

Soyinka ya kuma shawarci sauran jihohin da ke makwabtaka, a matsayin hadin kai, su ma su shiga zanga-zangar tare da rufe jihohinsu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel