2023: Ministan Buhari ya yi alfahari, ya ce APC na da abin da za ta rike don ci gaba da shugabancin kasar

2023: Ministan Buhari ya yi alfahari, ya ce APC na da abin da za ta rike don ci gaba da shugabancin kasar

- Gabanin babban zaben 2023, wani mamba a jam’iyyar APC ya nuna kwarin gwiwa kan jam’iyyar mai mulki

- A cewar Timipre Sylva, APC za ta ci gaba da rike kujerar shugaban kasar a zabe na gaba

- Sylva ya bayyana cewa babu wata jam'iyyar siyasa a Najeriya da ta fi APC karfi

Karamin Ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce mafi ingancin cin zaben shugabancin kasa a 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels Television a ranar Litinin, 8 ga watan Fabrairu.

Sylva ya lura cewa duk da matsalolin cikin gida da ke damun jam'iyyar mai mulki, ya nuna kwarin gwiwar cewa APC ce jam'iyya daya tamkar da dubu.

Ya kuma tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ci gaba da rike shugabancin kasar a shekarar 2023.

2023: Ministan Buhari ya yi alfahari, ya ce APC na da abin da za ta rike don ci gaba da shugabancin kasar
2023: Ministan Buhari ya yi alfahari, ya ce APC na da abin da za ta rike don ci gaba da shugabancin kasar Hoto: @HETimipreSylva
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC

Ministan ya ci gaba da cewa babu wata jam’iyyar siyasa da ta fi karfin APC a kasar nan a yau.

Ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya maida APC daban da sauran jam’iyyun kasar.

Wannan ci gaban na zuwa ne sama da mako guda bayan karamin ministan albarkatun man fetur, ya sake sabonta rijistarsa na dan jam'iyyar APC mai mulki a sabon rijistar da ke gudana a fadin kasar.

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode zai yuwu yana kan hanyarsa ta komawa jam'iyya mai mulki ta APC bayan kwashe shekaru 6 da yayi da barin PDP.

Majiyoyi kusa da shi sun sanar da The Nation yadda ya samu ganawa da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buuni tare da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano

Ganawar sirrin wacce ta dauka tsawon sa'a daya, an gano cewa tana da alaka da shirin komawar tsohon ministan jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel