Da duminsa: Femi Fani Kayode yana shirin komawa jam'iyyar APC

Da duminsa: Femi Fani Kayode yana shirin komawa jam'iyyar APC

- Femi Fani-Kayode yana shirin komawa jam'iyya mai mulki ta APC kamar yadda majiya makusanciya garesa ta tabbata

- A yau Litinin, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya yi ganawar sirri da Mai mala Buni tare da Gwamnan Kogi

- Majiyar ta tabbatar da cewa ganawar sa'a dayan bata rasa alaka da kokarin komawar Kayode jam'iyyar APC

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode zai yuwu yana kan hanyarsa ta komawa jam'iyya mai mulki ta APC bayan kwashe shekaru 6 da yayi da barin PDP.

Majiyoyi kusa da shi sun sanar da The Nation yadda ya samu ganawa da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buuni tare da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.

Ganawar sirrin wacce ta dauka tsawon sa'a daya, an gano cewa tana da alaka da shirin komawar tsohon ministan jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina

Da duminsa: Fani Kayode yana yunkurin komawa jam'iyyar APC
Da duminsa: Fani Kayode yana yunkurin komawa jam'iyyar APC. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Tun kafin nan, Fani-Kayode ya gana da Gwamna Bello a gidansa da ke Wuse Zone 6 a Abuja kafin su garzaya zuwa gidan saukar bakin Gwamna Mai Mala Buni.

KU KARANTA: 2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande ke sukar sabunta rijista da APC ke yi

A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel