Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC

Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC

- Martani na ci gaba da billowa daga shirye-shiryen da ake ikirarin Cif Femi Fani-Kayode na yi na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

- Ga dukkan alamu mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad bai ji dadin labarin ba

- Mai ba gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin yada labarai ma ya nuna rashin jin dadinsa game da labarin da ke tashe a yanzu

Rahotannin kafafen yada labarai a ranar Litinin, 8 ga watan Fabrairu sun nuna cewa tsohon ministan jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode na kan hanyarsa ta komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Rahotannin sun zama batun da ake ta tattaunawa bayan hotunan tsohon ministan da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello sun bayyana a kafafen sada zumunta.

Baya ga hotunan Fani-Kayode da Bello, wani hoto na shugabannin biyu tare da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya sake bayyana.

Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC
Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC Hoto: @realFFK
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter

Buni shine Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar mai mulki.

Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, ya nuna rashin jin dadinsa ga rahoton.

Ya rubuta a shafin Twitter:

"Idan ya yanke shawarar dawowa jam'iyyar mai mulki, bana tunanin zai samu karbuwa daga mafi yawan mambobin jam'iyyar, wadanda ya mayar da sukarsu da tozartasu aiki tsawon shekaru da dama."

Mai ba gwamnan jihar Kano shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai shi ma ya nuna kyamar sa game da labarin da yayi fice.

Ya rubuta:

“A gaskiya bana tunanin na fahimci sararin siyasar Najeriya kuma. Menene wannan kuma dan Allah? "

KU KARANTA KUMA: Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano

A baya mun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode zai yuwu yana kan hanyarsa ta komawa jam'iyya mai mulki ta APC bayan kwashe shekaru 6 da yayi da barin PDP.

Majiyoyi kusa da shi sun sanar da The Nation yadda ya samu ganawa da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buuni tare da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.

Ganawar sirrin wacce ta dauka tsawon sa'a daya, an gano cewa tana da alaka da shirin komawar tsohon ministan jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng