Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano

Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano

- Sanata Abba Moro na son a saki Elijah Odeh, wani mai aski da aka kama a jihar Kano

- Odeh memba ne na mazabar Moro, yankin Benuweta Kudu

- Dan majalisan na jihar Benuwe ya yi zargin cewa an hana mazabar sa beli

Sanata Abba Moro ya bukaci a saki Elijah Odeh, wani matashin mai aski da aka kama a jihar Kano kan salon askin da ya saba wa Musulunci, jaridar The Punch ta ruwaito.

Dan majalisan da ke wakiltar yankin Benuwe ta Kudu a majalisar dokoki ta kasa a cikin wata sanarwa daga ofishin yada labaransa a ranar Lahadi, 7 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa Odeh ya fito ne daga mazabarsa.

KU KARANTA KUMA: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa

Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano
Sanata ya bukaci kotu ta saki mai yi wa samari askin banza a Kano Hoto: @comic_undispute
Asali: Twitter

A cewar Maro, wata kungiyar Musulmai ce ta kama mai askin kan ikirarin cewa yana askin da ake ganin sun saba wa addinin Musulunci da kuma Annabi Muhammad (SAW).

Ya ci gaba da bayyana cewa a halin yanzu ana shari’ar mai askin a Kotun Majistare ta Gyadi-Gyadi da ke zaune a jihar Kano.

Dan majalisar ya kuma bayyana cewa duk da tsoma bakin da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, da takwaransa na jihar Kano Abdullahi Ganduje suka yi, ba a bayar da belin Odeh ba.

Ya ce wannan matakin tauye hakkin matashin ne na zama da yin kasuwanci a kowane bangare na kasar nan ba tare da tsangwama da musgunawa ba.

KU KARANTA KUMA: Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter

A gefe guda, wani matashi dan shekaru 23 da ake zargi da fashi da makami, Michael Ogungbade, wanda aka kama saboda ya afkawa mutane a yayin zirga-zirga ya yi ikirarin shiga aikata laifin sakamakon rashin aikin yi, Daily Trust ta ruwaito.

Ogungbade na daga cikin mutane 27 da ake zargi da aikata laifi da jami’an ‘yan sanda suka kama a Legas wadanda suka kai farmaki maboyarsu a cikin tsakiyar birnin Legas.

Samamen ya biyo bayan korafe-korafen hare-hare kan mutanen da ke kan ababen hawa yayin da suke cikin zirga-zirga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel