An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa

An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa

- Yan sanda a jihar Adamawa tare da hadin kan 'yan banga da mafarauta sun samu nasarar kashe 'yan fashi

- Sun kuma samu nasarar kame daya daga cikin 'yan ta'addan a yayin farmakin

- 'Yan sandan sun bayyana cewa suna kan bincike kan yadda za agurfanar da dan fashin

Wani farmaki da wasu jami'an 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta a jihar Adamawa suka kai wa mambobin kungiyar 'yan fashi ya yi sanadiyyar kashe biyu daga cikin 'yan fashin tare da kame daya.

Sauran mambobin kungiyar sun tsere bayan an ci karfinsu a farmakin, wanda ya faru da sanyin safiyar Litinin a kusa da karshen Numan na Babbar Hanyar Numan zuwa Jalingo, The Nation ta ruwaito.

DSP Suleiman Nguroje a jihar ta Adamawa, ya ce a cikin wata sanarwa da safiyar Litinin din da ta gabata an fara gudanar da aikin tsaro cikin nasara bisa umarnin kwamishinan 'yan sanda, CP Aliyu Adamu.

"Bayan wani mutumin kirki" ya ba da rahoton cewa wadanda ake zargi da fashi suna barna.

KU KARANTA: Wata 1 da aurensa, 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe matashin jami'in Soja

An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa
An harbe 'yan ta'adda biyu tare da kame daya a jihar Adamawa Hoto: The Guardian
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa aikin tsaro, wanda DPO mai kula da Numan Division ya jagoranta, ya sami nasarar saboda DPO ya yi sauri wajen tattara mutanensa da mambobin kungiyar sa-kai da kungiyar mafarauta.

A cewarsa, an kwato bindigogin, da wukake masu kaifi, adduna da layu daga wadanda ake zargin a daidai lokacin da aka damke daya daga cikinsu, Ashidu Balari, mazaunin Lafiya a karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa tare da raunin da ya samu daga harbe-harben.

“Wanda ake zargin wanda yanzu haka yake karbar kulawar asibiti ana bincikar shi dangane da makircin laifuka da fashi da makami.

“A halin yanzu, Rundunar 'yan sanda ta yaba wa jami’an ‘yan sanda na Numan Division saboda matakin da suka dauka na gaggawa wanda ya haifar da nasarorin da aka samu."

Karshe hukumar 'yan sanda ta bayyana cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zaran an kammala bincike,” in ji Nguroje.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an kula da dokar Korona 2,000

A wani labarin, An ceto matasa Takum 24 daga cikin 25 da masu satar mutane suka sace a hanyar Wukari - Takum a jihar Taraba.

Daily Trust ta tattaro cewa rundunar hadin kai na sjoji da 'yan sanda daga Benue da Taraba sun samu nasarar kubutar da matasan ne a wani samame da suka kai a cikin dazuzzukan da ke jihohin Taraba da Benue awanni kadan da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel