Wata 1 da aurensa, 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe matashin jami'in Soja

Wata 1 da aurensa, 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe matashin jami'in Soja

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe wani matashin ango a harin da suka kai Dikwa

- Matashin da yayi aure a watan Disamban bara, ya mutu tare da wasu sojoji a harin

- Majiya ta bayyana cewa bai samu damar halartar auren ba kasancewar yana kan aiki

'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe wani sojan Najeriya, a jihar Borno mai suna Abdullahi Bhuwa Usman.

Sahara Reporters ta gano cewa Usman yana cikin sojojin da aka kashe lokacin da maharan suka yi artabu da sojojin Najeriya a yakin da suka kwashe sa’o’i hudu don karbe garin Dikwa.

Harin ya faru ne ‘yan sa’o’i kadan bayan Laftanar Janar Tukur Buratai ya mika mukaminsa ga Manjo Janar Ibrahim Attahiru a matsayin Shugaban hafsan soji.

Rikicin ya fara ne da misalin karfe 6:00 na yamma kuma ya ci gaba har zuwa misalin karfe 10:00 na dare. Ya yi sanadin asarar rayuka da dama, ciki har da Usman.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa

'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sabon angon sojan Najeriya
'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sabon angon sojan Najeriya Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

"Na samu labarin mutuwar Usman cikin matukar kaduwa. Ya dai yi aure ne a ranar 27 ga Disamba, 2020. Na halarci daurin auren a nan Legas.

"Duk da cewa bai halarci bikin ba saboda yana bakin aiki, danginsa da abokansa duk sun kasance a nan suka tafi da matar zuwa jihar Borno a ranar.

"Har yanzu na yi magana da shi a makon da ya gabata kuma na gaya masa ya kula da matarsa; abin bakin ciki ne sosai. Yana da fara'a da kulawa," wani dangin mamacin ya fada wa SaharaReporters.

Harin ya faru ne kusan kwanaki biyar bayan da ‘yan bindigar suka yi amfani da bama-bamai bakwai a kan ayarin sojojin Najeriya na Sojojin Sama masu sulke da wasu motoci, wadanda ke karkashin rakiyar sintiri a Gorgi da ke Jihar Borno.

A cewar majiyoyin soji, sama da sojoji 30 aka kashe a yayin kwanton baunar.

‘Yan bindigar sun kuma lalata motoci uku da wata motar sulke.

KU KARANTA: Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne

A wani labarin, Sabbin hafsoshin sojan Najeriya sun isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno tare da niyyar ganawa da masu ruwa da tsaki don shawo kan yadda za a magance tayar da kayar baya a fagen daga.

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugabannin hafsoshin zuwa hedikwatar rundunar tsaro ta rundunar Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel