Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an kula da dokar Korona 2,000

Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an kula da dokar Korona 2,000

- Gwamnan jihar Kano ya kaddamar da wasu jami'an don kula da ka'idojin Korona

- Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na rage yaduwar cutar a jihar

- Ya kuma kirayi da su daure wajen bin ka'idojin Korona don samun nasarar yaki da cutar

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da wasu jami'ai 2,000 na COVID-19 domin fadakarwa tare da aiwatar da ladabi kan tsaro a jihar, PM News ta ruwaito.

Ganduje ya ce a lokacin kaddamarwar a Kano ranar Lahadi cewa akwai bukatar a magance COVID-19 da dukkan kokari da za a iya yi.

Ya kara da cewa an gano rashin bin ka’idoji na kare lafiya a matsayin babban kalubale ga dakile yaduwar kwayar.

Gwamnan ya lura da cewa, jami'an, wadanda suka hada da ma’aikatan kiwon lafiyar muhalli, za su yi aiki tare da hukumomin tsaro, jami’an tsaro da kotunan tafi da gidanka a cikin jihar don tabbatar da kiyaye duk wasu ka'idoji na COVID-19.

KU KARANTA: Wani dan majalisa ya harbe wanda ake zargin dan fashi da makami ne

Kano: Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an Korona 2,000
Kano: Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an Korona 2,000 Hoto: The News Nigeria
Asali: UGC

Ya ce, "babban kalubalen da muke fuskanta shi ne rashin bin ka’idoji na COVID-19 da jama'a ke bayarwa kuma mun shiga wayar da kan jama'a, amma dole ne gwamnati ta dauki matakan amfani da hukumomin tsaro da na mashal don tabbatar da kiyaye ka'idoji."

Kwamishinan lafiya, Aminu Tsanyawa, ya ce jihar ta samu mutane 27 da suka rasa rayukansu a karo na biyu kuma mutane 77 suka mutu tun barkewar cutar a jihar.

Tun da farko, mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya yaba wa gwamnan jihar kan kokarin da yake yi na yakar COVID-19 a jihar.

Ya shawarci jami'an da su fadakar da jama'a kan bin ka'idojin coronavirus.

Ado-Bayero ya yi kira ga mutanen jihar da su bi dukkan ka'idojin kiyaye lafiya.

Daga nan basaraken ya yi addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai, da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.

KU KARANTA: Sabbin hafsoshin sojoji sun isa Maiduguri don magance rashin tsaro

A wani labarin, Likitocin lafiya uku sun mutu yayin da wasu 53 suka kamu da kwayar ta COVID-19 tun bayan bullar kwayar cutar a jihar Kano, in ji Dakta Usman Ali, shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Daily Trust ta ruwaito.

Usman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce mutuwar ta kwanan nan ta wani kwararrun masanan cututtukan da suka mutu a wata cibiyar keɓewa a ranar Litinin a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel