Boko Haram: MNJTF sun yi galaba yayin da ‘Yan ta’adda suka kifar da Amir Abba Gana

Boko Haram: MNJTF sun yi galaba yayin da ‘Yan ta’adda suka kifar da Amir Abba Gana

- A ranar Juma’a, sojoji sun yi samame sun kashe wasu ‘Yan ta’adda a Borno

- Dakarun sojojin MNJTF sun hallaka manyan jagororin Boko Haram a harin

- ‘Yan Boko Haram sun yi bore, sun kifar da shugabansu a Tumbum Kayowa

A yunkurin da dakarun hadin-gwiwa su ke cigaba da yi na ganin bayan ‘yan ta’adda, sun halaka wasu manyan jagororin kungiyar Boko Haram.

Jaridar PRNigeria ta fitar da rahoto cewa sojojin MNJTF sun yi samame a ranar Juma’a, 29 ga watan Junairu, 2021, inda su ka samu galaba a kan Boko Haram.

Rahoton ya tabbatar da cewa a wannan samame da aka kai, sojojin sun hallaka wasu manyan jagororin Boko Haram biyu; Alai Bor da Maleum Modu.

Bayan haka, sojojin sun kashe mayakan kungiyar ta’addan Boko Haram a yankin na Arewa maso gabas.

KU KARANTA: Sabon hafsun tsaro ya gargadi Abubakar Shekau

“Dakarun Najeriya da hadin gwiwar MNJTF sun kashe Alai Bor, shugaban Boko Haram a kauyen Buwari, a garin Bama, yayin da yake yunkurin tsallaka wa Gwoza-Pulka.”

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar hallaka wasu mayaka shida da ke cikin tagawar Amir Bor.

"Sauran jagororin ‘yan ta’adda, Maleum Modu da kuma mayakan Boko Haram uku sun mutu a hannun dakarun sojojin da ke sintiri a yankin Mafa.”

Hakan na zuwa ne bayan wasu mayakan ta’addan sun yi juyin-mulki, sun hambarar da gwamnatin Amir Abbah-Gana Tumbum Kayowa, inda aka yi jina-jina.

KU KARANTA: Gwamna da Sarkin Daura sun tarbi jirgin Buhari a Katsina

Boko Haram: MNJTF sun yi galaba yayin da ‘Yan ta’adda suka kifar da Amir Abba Gana
Janar I. Attahiru da T.Y Buratai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

‘Yan ta’addan sun kifar da Abbah-Gana ne bayan zanga-zangar da aka yi masa a dalilin nada Aliyu Chakkar da ya yi a matsayin gwamnan Tafkin Chadi bayan Goni Maina.

Kwanakin baya kun samu rahoto cewa daga zuwa gidan biki, miyagu masu satar jama’a sun yi garkuwa da wasu matasa 25 a karamar hukumar Takum, Jihar Taraba.

Wadannan 'yan bindiga sun ce sai an biya Naira Miliyan 50 za a fito da wadannan matasa da aka sace a hanyar zuwa biki, inda aka bukaci kowa ya biya miliyan biyu.

Daga baya an fito da duka wadannan Bayin Allah, bayan sun shafe kwanaki kusan uku a tsare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel