Buhari ya bar Abuja, ya isa garin Daura domin yin rajistar Jam’iyyar APC

Buhari ya bar Abuja, ya isa garin Daura domin yin rajistar Jam’iyyar APC

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara zuwa mahaifarsa, Daura

- Garba Shehu ya ce Buhari ya je gida ne domin ya yi rajistar Jam’iyyar APC

- A ranar Talata mai zuwa Shugaban Najeriyar zai koma birnin tarayya Abuja

A yau Juma’a, 29 ga watan Junairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dura garin Daura, mahaifarsa, inda ake sa ran zai shafe ‘yan kwanaki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin mai girma Muhammadu Buhari ya sauka ne ta babban filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke jihar Katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Munir Yakubu, shugaban majalisar dokokin Katsina, da Alkalin Alkalan jihar su ka tarbi shugaban kasar.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Facebook da yammacin yau.

KU KARANTA: Buhari zai je Daura yau

Garba Shehu ya bayyana cewa Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar, ya jagoranci sauran hakimai da sarakan Daura su ka tarbi jirgin da ya kawo Buhari.

“A zamansa da zai yi a Daura, ana sa ran zai yi wasu abubuwa, daga ciki har da yin rajistar zama ‘dan APC da aikin tabbatar da zama ‘dan jam’iyya.” Inji Shehu.

Jawabin ya ce: “shugaban kasar ya na ganin muhimmancin wannan aiki ga damukaradiyyar kasar nan da yunkurin kawo shugabanci na gari wajen cigaban kasa.”

Shehu ya ce ana sa ran Muhammadu Buhari zai koma babban birnin tarayya a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021, domin cigaba da ayyukan da ke gabansa.

Buhari ya bar Abuja, ya isa garin Daura domin yin rajistar Jam’iyyar APC
Rajistar zama ‘Dan APC ta dauke Buhari daga Abuja Hoto; @BashirAhmaad
Asali: Twitter

KU KARANTA: An karrama Buratai a Abuja

Wannan ne karo na biyu da shugaban kasar ya zo Daura a ‘yan kwanakin, ya kai ziyara zuwa gida a watan Disamba, inda ya shafe kusan mako guda kafin ya koma.

Yayin da ya kai ziyara zuwa gida lokacin, wani bidiyon shugaba Muhammadu Buhari ya na duba dabbobinsa ya karade shafukan gizo, ya kuma jawo surutun mutane.

A wannan lokaci ne aka shiga wata makarantar gwamnati a garin Kankara, aka sace dalibai 300

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel