Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro

- Dan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi martani kan nadin sabbin hafsoshin tsaro

- Shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaro ranar Alhamis

- Shekau ya ce babu abinda sabbin Sojojin zasu tsinana

Shugaban yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon jawabin cewa, babu abinda sabbin hafsoshin tsaron zasu tsinana kamar yadda magabatansu sukayi wajen yaki da ta'addanci a Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakazalika Shekau ya yi kira ga sabon shugaban hafsoshin tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, ya tausayawa kansa, ya tuba kuma ya Musulunta.

Shekau, wanda yayi magana na tsawon mintuna goma, ya yi kira ga sabon shugaban hafsan Sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya sani cewa abubuwan da yake yi ya sabawa addinin Musulunci, saboda haka ya kafurta.

A cewar Shekau, zasu kai sabbin hare-hare a kasar, kuma yan Najeriya su daina tunanin sabbin hafsoshin ba zai haifi da mai ido ba.

Za ku tuna cewa sabon shugaban hafsoshin tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor da sabon shugaban Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru sun jagoranci yaki da yan ta'addan Boko Haram karkashin atisayen Operation Lafiya Dole.

KU KARANTA: Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu

Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro
Ka tuba kuma ka Musulunta, Shekau ga sabon shugaban hafsan tsaro Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

DUBA NAN: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

A bangare guda, tsohon hafsin sojan kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai mai murabus, ya ce ya gyara harkar sojin Najeriya fiye da yadda ya sameta.

Ya furta hakan ne a wani taron faretin saukarsa daga kujerarsa a ranar Juma'a a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Ya kara da cewa ya tabbatar da cewa ya bai wa sojojin cikakkiyar horarwa da kuma inganta walwalarsu.

Kamar yadda yace "Yau ranar farinciki ce ba ta takaici ba, saboda zan yi murnar barin sojojin Najeriya fiye da yadda na same su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng