Taraba: Miyagun da su ka yi garkuwa da samarin Takum sun ce a biya N52m

Taraba: Miyagun da su ka yi garkuwa da samarin Takum sun ce a biya N52m

- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu samari a Takum

- Miyagun sun tsare wadannan mutane ne su na dawowa daga wani biki

- Mummunan lamari ya auku ne tsakanin Wukari da Takum a Taraba

Miyagun ‘yan bindigan da su ka sace matasa 25 da direba 'yan garin Takum, jihar Taraba, sun bukaci a biya makudan miliyoyin kudi kafin su fito da su.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan bindigan sun sa Naira miliyan 52 a matsayin sharadin sakin wadannan Bayin Allah da aka sace a ranar Laraba.

Wani daga cikin iyalin wadanda aka sace ya yi magana da manema labarai ta wayar salula a ranar Juma’a, ya ce ‘yan bindigan sun nemi kudi a hannunsu.

Kamar yadda wannan mutum ya bayyana, masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan biyu a kan kowane mutum a lokacin da su ka tuntube su.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka 'Yan bindiga a Kaduna

A cewarsa, an yi gaba da matasan da aka tare a hanya tare da direbansu ne zuwa wani kungurmin daji tsakanin Taraba da Katsina-Ala, a jihar Benuwai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar wa manema labarai cewa an yi magana da ‘yan bindigan.

DSP David Misal ya yi kira ga matasan garin Takum, su yi hakuri, ya yi alkawari cewa jami’an tsaro za su yi bakin kokarinsu na ceto wanda aka tsare.

Har zuwa yanzu da mu ke tattara wannan rahoto, wadannan mutane da aka tsare su na hannu.

KU KARANTA: Babu wanda ya yi wa matasa irin hidimar da Buhari yake yi – Sanatan Borno

Taraba: Miyagun da su ka yi garkuwa da samarin Takum sun ce a biya N52m
Gwamnan Taraba, Darius Ishaku Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

Da alama ‘yan bindigan su na sa ran samun N50m daga hannun matasan da ke cikin wannan mota da aka tare, sai kuma N2m daga hannun direban motar.

A yau kun ji cewa ‘yan bindiga a Najeriya sun kashe mutane akalla 18, hakan na zuwa ne jim kadan bayan an nada sababbin shugabannin sojoji a kasar.

Kun ji cewa a jihar Taraba, matasa rututu aka yi gaba da su yayin da su ke dawo wa daga bikin daurin aure a kan hanyar Wukari zuwa Takum, har yanzu shiru.

Wadannan hare-haren da aka kai a Kaduna, Katsina, Neja da Taraba ya ci mutum kusan 100.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel