Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno

Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno

- Gwamnan jihar Borno ya sake bada umarnin kara daukan likitoci don inganta asibitocin jihar

- Gwanman a baya ya ba da umarnin daukar ma'aikatan lafiya sama da 500 a jihar

- Gwamnanatin jihar ta kuma sayi wani fili a gaban wani asibiti don rage cunkoso a asibitin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Talata ya ba da umarnin daukar likitoci 40 a matsayin kari kan yardarsa da ya yi a baya, domin biyan bukatun kula da lafiya na karuwar al’ummar jihar, Vanguard News ta ruwaito.

Shawarwarin na ranar Talata na zuwa ne watanni hudu bayan da Gwamnan ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 594.

Daga cikin wadanda za a dauka sun hada da: likitoci lafiya 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozomomi, masu harhada magunguna 45 da kwararrun masana kiwon lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi.

KU KARANTA: Ahmad Lawan ya bai wa gwamnati shawarin ta daina bijiro da uzuri

Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno
Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno Hoto: Vanguard News
Source: UGC

Zulum ya sanar da amincewarsa ta baya-bayan nan ga daukar likitoci 40 bayan taron na ranar Talata tare da shugabannin gudanarwa na asibitocin gwamnati bakwai da cibiyoyin da ke da alaƙa da ke Maiduguri Metropolitan Council da ƙaramar hukumar Jere.

Taron, wanda aka gudanar a sirrance, ya ta'allaka kan inganta tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da inganci da isar da aiyuka ga 'yan kasa daidai da manufofin gwamnatin Zulum.

Bayan taron, Gwamna Zulum ya gudanar da aikin duba asibitin na Kwararru sannan ya ba da umarnin gina wani sashe domin rage yawan cunkoso a wasu wuraren.

KU KARANTA: Matsi ya sa wasu direbobi bude tasha mai suna Tashar Buhari

Gwamnan ya kuma duba wani fili da Gwamnatin Jihar Borno ta saya da ke gaban asibitin kwararru, wanda za a yi amfani da shi domin fadada asibitin.

A wani labarin, Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya sanya yara 1,163 na mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a wata makaranta a garin da aka kwato daga hannun masu tayar da kayar baya a jihar, The Sun ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya sanya ido a kan sanya yara 'yan gudun hijirar a garin Damasak, a ranar karshe ta ziyarar da ya kai yankin ranar Litinin, ya ce atisayen wani yunkuri ne na tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su shiga makarantu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel