Bani da N50m kudin fansa - mahaifn 'ya'ya 7 da a ka sace
- Shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara ya bayyana bai da kudin fansar 'ya'yansa da a ka sace
- Shugaban ya nuna adawarsa da biyan kudin fansa ga masu satar mutane
- Jigon jam'iyyar ya kuma bayyana cewa ya mayar da al'amarinsa ga Allah kan 'ya'yan nasa
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Alhaji Sani Gyare, ya ce bashi da kudin fansa N50m da masu satar mutane ke nema domin sakin yaran sa guda bakwai.
An sace yaran Gyare su bakwai a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da ‘yan bindiga suka afka gidan su da ke Maru. Yaran su ne Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyan, Armaya’u da Mubarak.
KU KARANTA: Da duminsa: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona
Da yake magana da jaridar Sunday Tribune a ranar Asabar, jigon jam'iyyar ya bayyana cewa yana adawa da biyan kudin fansa.
"Dole ne mu daina biyan kudin fansa saboda irin kudin da 'yan daba ke amfani da su wajen sayen karin alburusai don haifar da rikici a cikin al'ummomin mu."
Ya kara da cewa: “Gaskiya ba ni da irin wadannan kudin.
"Za ku iya ganin irin wannan kuɗin ne kawai idan kun je banki ko daga attajiran da ke kusa. A gare ni ina fata da addu'a cewa, yarana za su dawo ba tare da rauni ba. Tun lokacin da na yi magana da su [masu garkuwar], ba su sake kira ba.
KU KARANTA: Babu cutarwar da za ta sami Bishop Kukah - CAN
“Gaskiya na yi asara saboda ban san ta inda zan fara ba; abin da zan fada musu ko nawa zan biya kafin a sako ’ya’yana,” Gyare ya koka.
A wani labarin daban, A ranar Asabar ne rundunar Operation Hadarin Daji, ta fatattaki 'yan ta'adda akalla 50 a kauyen Kuriya da ke karamar hukumar Kaura Namoda a Zamfara, in ji hedkwatar tsaro.
Mai Gudanarwa a Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. John Enenche ya fada cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa sojojin sun kuma kwato dabbobi 334 da barayin suka sace a yayin arangamar, Daily Trust ta ruwaito.
Enenche ya ce sojojin sun yi nasarar ne tare da taimakon saojin sama.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng