"Alkaluma sun nuna bai dace in amince na sha kashi ba" Inji Donald Trump

"Alkaluma sun nuna bai dace in amince na sha kashi ba" Inji Donald Trump

- An tambayi mutanen Amurka game da sakamakon zaben shugaban kasa

- 98% na Amurka da suka shiga zaben ba su goyon bayan Trump ya hakura

- Donald Trump ya bayyana wannan, kila ya kara kwarin gwiwar zuwa kotu

Alkaluma sun tabbatar da cewa da-dama na mutanen kasar Amurka basu goyon bayan shugaba Donald Trump ya yarda ya fadi zaben da aka yi.

Wani gidan yada labarai ya gudanar da bincike, wanda sakamakonsa ya nuna akasarin jama’a, kusan mutum 200, 000 suna tare da Donald Trump.

Da aka tambayi jama’a ko sun yarda shugaba Donald Trump ya yi na’am da sakamakon zabe da ke nuna Joe Biden ya yi nasara, da-dama sun ce a’a.

KU KARANTA: Aminai sun ba Trump shawarar ya hakura, ya sake takara a 2024

A cikin mutanen da su ka kada kuri’arsu a wannan zabe na jin ra’ayi da aka gudanar, mutane 2, 181 ne kacal su ka nemi Trump ya rungumi kaddara.

Ragowar mutane 192, 774 wanda ke nufin 98% na wadanda su ka bayyana ra’ayinsu, sun zabi shugaban Amurkan ya kalubalanci sakamakon zaben.

“Shin Trump ya sallama cewa Biden ya doke shi? A’a: 190,593 (98.9%); Eh: 2,181 (1.1%) Yawan kuri’u: 192, 774.”

Donald Trump ya rubuta: “Dole muyi nasara domin cigaban kasarmu.

KKU KARANTA: Mutumin Abia ya shiga cikin Turawa domin gano maganin Coronavirus

Alkaluma sun nuna bai dace in amince na sha kashi ba inji Donald Trump
Biden da Shugaba Trump Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A zaben da aka gudanar a karshen bana, Trump da jam’iyyarsa mai-ci ta Republican, sun sha kashi a hannun ‘dan takarar adawa, Joe Biden mai shekara 68.

Donald Trump ya fara shirin mika ragamar kasar Amurka ga shugaba mai-jiran-gado Joe Biden, amma har yanzu Trump bai yarda an doke shi a zaben bana ba.

Jim kadan bayan an kammala zabe, shugaban Amurkan, Donald Trump ya ce bai amince da nasarar da ake ganin abokin hammayarsa Joe Biden ya samu ba.

Donald Trump ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su sanar da wanda ya lashe zaben ba. A karshe dai haka aka yi, aka tabbatar da nasarar jam'yyar adawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng