Trump ya yi watsi da nasarar Biden, ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su zabi shugaban kasa ba

Trump ya yi watsi da nasarar Biden, ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su zabi shugaban kasa ba

- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai amince da nasarar da ake ganin abokin hammayarsa Joe Biden ya samu ba

- Trump ya ce ba kafafen watsa labarai ne ke sanar da wanda ya lashe zabe ba don haka har yanzu ba a gama zabe ba

- Har wa yau, Trump ya yi ikirarin cewa akwai matsala tattare da zaben inda ya ce an hana wakilan jam'iyyarsa masu saka ido shiga wurin kirga kuri'u a Pennsylvania

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ki amincewa da nasarar zabebben shugaba Joe Biden.

Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter jim kadan bayan da kafafen watsa labarai suka ambaton nasarar tsohon mataimakin shugaban kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Dan takarar na jam'iyyar Republican Party ya ce an tafka kure-kurai da dama a zaben don haka zai garzaya kotu a ranar Litinin don kallubalantar sakamakon zaben.

Trump ya yi watsi da nasarar Biden, ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su zabi shugaban kasa ba
Trump ya yi watsi da nasarar Biden, ya ce ba kafafen watsa labarai ne za su zabi shugaban kasa ba. Hoto: Chip Somodevilla/ Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Ya ce, "Dukkan mu mun san dalilin da yasa Joe Biden ke gaggawan nuna kansa a matsayin wanda ya yi nasara, da kuma dalilin da yasa abokansa na kafafen watsa labarai ko kokarin ganin sun taimaka masa: Ba su son gaskiya ta bayyana. Maganar gaskiya ita ce har yanzu ba a gama zabe ba."

Trump ya ce ba a tabbatar da Biden a matsayin dan takarar da ya lashe zabe a ko jiha guda ba.

KU KARANTA: An yi wa 'yar gidan sarautar Saudiyya fashi

Shugaban kasar ya ce an hana wakilan jam'iyyarsa masu saka ido kan zabe su shiga wurin da ake kidaya kuriu a Jihar Pennsylvania wacce itace jihar da ta bawa Biden nasararsa ta karshe.

A wani labarin, kungiyar malam jami'a (ASUU) a ranar Juma'a ta roki gwamnatin tarayya ta taji tausayin yayan talakawan Najeriya, ta kuma gaggauta amincewa da bukatar domin kuwa sun gaji da yajin aiki.

Kungiyar tace gwamnati na matsa mata akan ta janye yajin aikin ne, saboda ganin irin barnar da matasa suka yi lokacin zanga zangar Endsars kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164