Rahotanni sun ce Donald Trump ya na la’akari da fitowa takara a 2024
- Rahotanni sun fara nuna Donald Trump na iya neman takara nan gaba
- Idan Shugaba Trump bai samu tazarce ba, zai nemi mulki a zaben 2024
- Tsofaffin Hadiman Shugaban kasar sun bijiro masa da batun tarar gaba
Rahotannin da ke fitowa su na nuna cewa shugaban kasa Donald Trump na iya sake jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa da za ayi a shekarar 2024.
Idan har Donald J. Trump ya sha kashi a zaben bana, ya na da damar ya fito takara a nan gaba.
Tazarcen shugaban kasar Amurka na 45 a tarihi, Donald Trump ta na fuskantar barazana a hannun ‘dan takarar jam’iyyar hamayya, Joe Biden.
KU KARANTA: Sakamakon zaben Amurka dalla-dalla
Da ya ke magana da ‘yan jarida, tsohon Hadimin Donald Trump, Bryan Lanza ya ce ya yi imani cewa shugaban kasar zai iya sake shiga takara.
“Kowa ya na maganar gagarumar nasara ne, mu ribanya abokin hamayya, mu na sa ran bada tazara a kuri’un ‘Collage’, amma ko kusa!’” inji Lanza.
Bryan Lanza ya ce idan ya samu dama, zai ba Trump shawara ya hakura yanzu, ya tsira da mutuncinsa, ya yi wata takarar nan da shekaru hudu.
Shi ma Steve Bannon, wanda ya yi aiki da Trump a baya, ya bayyana cewa ko da shugaban kasar ya sha kashi a zaben nan, hakan bai nufin karshensa.
KU KARANTA: Inda Najeriya da kasashen Afrika za su tsinci kansu mulkin Biden
Mulvaney ya ce ko da Trump zai yi takara a 2024, shekarunsa ba za su haura na Biden a yanzu ba.
Jihohin sun hada da Wisconsin, Michigan, Georgia, Arizona, Pennsylvania, Alaska, Nevada da North Carolina
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng