Ogbuagu ya na cikin Likitocin Pfizer dake binciken maganin cutar COVID-19

Ogbuagu ya na cikin Likitocin Pfizer dake binciken maganin cutar COVID-19

- Dr. Onyema Ogbuagu ya na cikin masu kokarin fito da maganin Coronavirus

- Ogbuagu ya na cikin Tagwayen da Farfesa Chibuzo Ogbuagu ya haifa a Abia

- Likitan ya kai matsayin mataimakin Farfesa kan ilmin cututtuka masu yaduwa

Mutumin Najeriya, Onyema Ogbuagu, ya jawo wa kasarsa abin alfahari dalilin aikin da ya ke yi na ceto rayukan mutum miliyan 20 da ke da COVID-19.

Haifaffen ‘dan Najeriya, Dr. Onyema Ogbuagu ya na cikin tawagar kwararrun likitocin dake bincike da nufin gano maganin cutar Coronavirus.

An haifi Onyema Ogbuagu wanda yanzu tare da wasu masana a karkashin kamfanin Pfizer suke kan hanyar gano maganin COVID-19 ne a jihar Abia.

KU KARANTA: Wasu Malaman Jami’a sun lallabo, su na shirin kishiyantar ASUU

BBC ta fitar da rahoto Ogbuagu ya na cewa maganin da suke aiki a kai ya yi tasiri a kan 94% na masu dauke da COVID-19 da su ka yi amfani da shi.

Likitan da yanzu taurauwarsa ta ke haskawa a ko ina shi ne darektan sashen Yale AIDS Program HIV da ke aiki a kan cutar kanjamau a jami’ar Yale.

Dr. Ogbuagu ya kasance ya na irin wannan aiki na gano magungunan cututtuka masu yaduwa.

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya yi magana inda ya bayyana alfaharin da jiharsa ta ke yi na ganin ‘danta ya na yin abin da zai ceci jama’a.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisar Ebonyi su yi maza-maza su tsige Gwamna Umahi – AESID

Ogbuagu ya na cikin Likitocin Pfizer dake binciken maganin cutar COVID-19
Dr. Onyema Ogbuagu Hoto: BBC.com
Asali: UGC

Okezie Victor Ikpeazu ya bayyana cewa bai yi mamaki da jin kokarin Likitan ba domin ya yi gado ne wajen mahaifinsa, Farfesa Chibuzo Ogbuagu.

Ofishin jakadancin Amurka ta yaba da aikin Onyema Ogbuagu, tsohon dalibin na jami’ar Calabar wanda daf ya ke da ya zama Farfesa a kasar Amurka.

Watanni shida da su ka wuce aka ji cewa wata kungiya ta masana a sashen hada magunguna na jami'ar ABU Zaria ta ce ta gano maganin COVID-19.

Daga lokacin da Farfesa Abdu Kaita ya ce sun samo maganin cutar na COVID-19 daga wasu tsirrai, har yanzu ba a sake jin labarin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel