Fashola: Tsarin kama-kama ya na cikin ‘alkawarin’ jam’iyyar APC da ba a rubuta ba
- Babatunde Raji Fashola ya na ganin Kudu ya kamata a kai tikiti a zabe na 2023
- Ministan ya ce tun da Arewa tayi mulki daga 2015, lokacin mutanen Kudu ya yi
- Ya ce akwai magana a kasa cewa za a rika zagayawa da kujerar shugaban kasa
A ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Babatunde Raji Fashola, ya yi magana game da siyasar 2023 a gidan APC.
Babatunde Raji Fashola SAN ya ce yadda tsarin kama-kama ya yi aiki a zaben 2015, ya kamata idan an zo 2023, a bar mulki ya koma wa yan yankin kudu.
Jaridar Daily Trust ta ce tsohon gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da wasu ‘ya ‘yan APC suke kokarin ganin an bar Arewa su cigaba da mulki.
KU KARANTA: Wasu Ministoci sun fara hangen kujerar Shugaban kasa a 2023
Ministan da yake tattauna wa da ‘yan jarida a Abuja, ya roki shugabannin jam’iyyarsu su bi tsarin da aka dauko wajen zaben yankin da zai yi takara a 2015.
Fashola ya ce ya kamata a bi tsarin da ake tafiya a kai ko da ba a rubuta alkawarin a matsayin yarjejeniya ba, ya ce da an yi hakan, to da magana ta kare.
“Amma ka da a karya alkawarin da ‘yanuwa su ka yi, dole a cika alkawarin nan.” Inji Fashola.
KU KARANTA: Gwamnonin APC da za su iya rike Najeriya a 2023
A cewar Raji Fashola, ‘ya ‘yan jam’iyya za su iya cewa yanzu ‘dan autan cikinsu ko mace ce za ta rike wata kujera, ya ce ko ba a rubuta ba, hakan ta zauna.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC mai mulki, Yekini Nabena ya shaida wa Punch cewa kafin zaben 2015, an tsara yadda za a yi takarar shugaban kasa.
Yekini Nabena yace shugabannin APC sun yarda a tsakaninsu cewa idan ‘dan Arewa ya gama mulki, za a mika tikiti ne zuwa yankin kudancin Najeriya.
Da alamu rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar APC mai mulki shi ne inda za a kai tikiti a 2023.
A ranar Litinin, darekta janar na kungiyar PGF, Dr. Salihu Lukman, ya ce APC za ta fara sayar da fom din takara, kuma ba a tsaida yankin da za a ba tikiti ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng