Garkuwa da mutane: Ana neman N270m a kan Daliban da aka yi awon gaba da su
- An tuntubi ‘yanuwan yaran da aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja
- ‘Yan bindigan su na neman Naira miliyan 30 a kan kowane dalibi guda
- Wani daga cikin daliban ABU Zaria da aka tare ya samu ya sha da kyar
Masu garkuwa da mutane sun sa kudin fansa a kan ‘daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da aka sace a kan hanyar zuwa garin Abuja.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa miyagu sun nemi a biya Naira miliyan 270 kafin su fito da wadannan ‘dalibai har tara da su ka tsare.
Wani daga cikin wadanda ‘yan bindigan su ka tsare, Dickson Oko, ya yi nasarar kubuta, ya kuma shaida wa manema labarai halin da ake ciki.
KU KARANTA: Shehu Sani ya yi magana kan yadda za a samu tsaro a hanyar Kaduna-Abuja
Mista Dickson Oko ya ce miyagun sun tuntubi ‘yanuwan ‘daliban da su ka tsare inda su ka bukaci kowanensu ya biya miliyan 30 a matsayin fansa.
Oko wanda ya aka yi wa rauni da bindiga a dalilin harin ya na samun sauki a yanzu, amma hankalinsa a tashe ya ke saboda tsare takwarorinsa.
Matashin ya shaida wa jaridar cewa ya na cikin wadanda su ka tsere a lokacin da ‘yan bindigan su ka tare su a kan hanyar su ta zuwa garin Abuja.
Mista Oko ya ce shi da direbansu mai suna Nuruddeen Mohammed sun ci kafar kare, inda har ya bar wayoyin salularsa da wasu kaya a cikin motarsu.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun aika Mai Unguwa da ‘Dansa lahira a Kaduna
Mutane 12 ne a wannan mota da ta dauko yaran makarantar, daga ciki an kama mutum tara.
Iyalan wata mace daga cikin ‘daliban sun fada wa VOA Hausa cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntube su, kuma sun bukaci miliyan 30 daga gare su.
Majalisa ta na so a kafa Hukumar da za ta rika yi wa tsofaffin ‘Yan Boko Haram dawainiya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng