Kaduna-Abuja: Da ‘dan gari a kan ci gari, a dauki matasa aikin tsaro inji Sani

Kaduna-Abuja: Da ‘dan gari a kan ci gari, a dauki matasa aikin tsaro inji Sani

- Shehu Sani ya yi magana game da rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Sanata Shehu Sani ya ba Gwamnati shawarar ta dauki ‘yan yankin aikin tsaro

- Tsohon ‘Dan Majalisar ya ce mutanen yankin za su fi iya shawo kan matsalar

Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin Kaduna.

Kwamred Shehu Sani ya ba gwamnatin tarayya shawarar cewa a dauki matasan da ke zaune a wuraren da ake ta’adin, a zuba su cikin jami’an tsaro.

“Maganin garkuwa da mutane a hanyar Kaduna-Abuja. Akwai kauyuka kusan 37 a kan titin . A dauki matasan kauyukan nan a zuba aikin ‘yan sanda da NSCDC.”

KU KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello

“Daga nan a tura su aiki zuwa kauyukan da su ka fito domin su tsare hanyar, su kuma yi maganin masu garkuwa da mutanen nan.” Inji Shehu Sani a Twitter.

Tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya karkare da cewa: “Sun fi sanin wuraren nan.”

Shehu Sani ya bada wannan shawara ne bayan ‘yan bindiga sun fito da rana tsaka sun tsare Bayin Allah a kusa da garin Rijana, a ranar Lahadi da yamma.

Kafin yanzu, Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya ce akwai bukatar sojojin Operation Puff Adder su dawo aiki.

KU KARANTA: Miyagu sun yi ta'adi a Kauyen Jihar Kaduna

Kaduna-Abuja: Da ‘dan gari a kan ci gari, a dauki matasa aikin tsaro inji Sani
Garin Abuja Hoto: stearsng.com
Asali: UGC

Da ya ke magana game da lamarin a ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba, 2020, Sani ya ce: “A nan ne ake bukatar gwamnonin Arewa.”

Sani ya kuma bayyana cewa an saci wasu daga cikin dalibar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a harin da 'yan bindiga su ka kai a hanyar Abuja.

Gwamnati za ta dauki dawainiyar tubabbun sojojin Boko Haram a kasar waje idan har wani kudiri da 'yan majalisa su ka kawo ya sam karbuwa.

Majalisar dattawa ta na so a kafa Hukuma da za ta rika yi wa ‘Yan Boko Haram da su ka tuba hidima.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel