Kaduna: ‘Yan bindiga sun aika Mai Unguwa da ‘Dansa lahira a Zangon Kataf

Kaduna: ‘Yan bindiga sun aika Mai Unguwa da ‘Dansa lahira a Zangon Kataf

- ‘Yan bindiga sun kashe wani Mai Unguwa a yankin Zangon Kataf a Kaduna

- Bayan haka, Miyagun sun harbe ‘dansa har lahira, sannan au bindige matarsa

- Har zuwa yanzu jami’an tsaro ba su iya kama wadanda su ka yi ta’adin nan ba

Daily Trust ta rahoto cewa ‘yan bindiga sun auka wa kasar Atyap a karamar hukumar Zangon-Kataf, jihar Kaduna, inda su ka hallaka wani Basarake.

Rahotanni sun bayyana cewa wadannan miyagun ‘yan bindiga sun kashe Mai garin Gidan Zaki, Haruna Kuyet.

Bayan haka, miyagun sun kashe ‘dan wannan Basarake, sannan sun harbi Mai dakinsa, yanzu haka wannan Baiwar Allah ta na asibiti inda ake duba ta.

KU KARANTA: Shugaba Buhari da Gwamnonin Jihohi sun ba Jama’a kunya – CNG

A wani rahoton, miyagun sun raunata wata daga cikin ‘ya ‘yan marigayi Haruna Kuyet. An kai masa hari ne har gida da tsakar dare a ranar Litinin dinnan.

Wani babban jamii’in gwamnati a karamar hukumar Zango Kataf, Elisha Sako, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun shiga Atyap, sun yi wannan aika-aika.

Mista Elisha Sako ya yi tir da wannan mummunan lamari, ya kuma bayyana cewa kawo yanzu hukuma ba ta gano miyagun da su ka yi wannan ta’adin ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun harbo jirgi a Borno

Kaduna: ‘Yan bindiga sun aika Mai Unguwa da ‘Dansa lahira a Zangon Kataf
Malam Nasir-El-Rufai Hoto: naija247news.com
Asali: UGC

Sako ya ce jami’an tsaro sun baza jama’a a yankin domin a cafke wadanda su ka kashe Basaraken.

Sunan ‘dan marigayin wanda aka kashe su tare shi ne Destiny Kuye. Gwamnatin Kaduna ta ce an samu makaman da ‘yan bindigan su ka yi amfani da su bayan harin.

Kwamishinan harkokin cikin gida na gwamnatin Kaduna, Samuel Aruwan ya ce an samu kwankwon alburusai a inda aka kai harin jiyan a cikin gidan Mai garin.

Dazu kun ji cewa Shehu Sani ya bada shawarar kawo karshen garkuwa da mutane a titin Abuja zuwa Kaduna, ganin yadda ake yawan addabar matafiya a hanyar.

Tsohon ‘Dan Majalisar ya ba gwamnati shawarar ta dauki mutanen yankin a aikin tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel