Najeriya ta kawo kudirin da zai sa a rika kai tsofaffin ‘Yan Boko Haram karatu
- An kawo kudirin kafa Ma’aikatar da za ta kula da tsofaffin ’Yan Boko Haram
- Majalisar dattawa ta na so a rika ba tubabbun ‘Yan ta’adda karatu mai nagarta
- Sanata Ibrahim Geidem ya kawo wannan kudiri da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasa
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a game da sabon kudirin da aka kawo a majalisa domin ilmantar da tsofaffin ‘yan ta’addan Boko Haram a Najeriya.
Wannan kudiri zai yi kokarin sauya tunanin tubabbun ‘Yan Boko Haram, sannan a ba su matsuguni.
Hukumomi irinsu UBEC da TETFund da gwamnatocin jihohin Arewa maso gabas ne za su kawo kudin da za ayi wa tubabbun ‘yan ta’addan hidima.
KU KARANTA: Barayi su ka kewaye Gwamnatin Buhari - Sanatan Borno
‘Yan majalisa sun kira wannan kudiri da: A Bill for the Establishment of the National Agency for the Education, Rehabilitation, De-radicalisation and Integration of Repentant Insurgents in Nigeria and for Other Connected Purposes’
A ranar Alhamis da ta gabata, aka saurari wannan kudiri a karon farko, har ya samu karbuwa. Amma kudirin na Ibrahim Geidem ya jawo surutu a waje.
Sanata Ibrahim Geidem ya bayyana dalilin kai wannan kudiri gaban majalisar dattawa, ya ce ‘yan Boko Haram da-dama su na da niyyar ajiye makamansu.
A cewar Sanatan na Yobe, wannan kudiri zai dauki dawainiyar ‘yan ta’addan da su ka ajiye kayan yaki ne, ba wadanda su ka shiga hannun jami’an tsaro ba.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun dawo titin Abuja, sun yi kashe-kashe
Shugaban kasa ne zai nada shugaba da zai kula da wannan ma’aikata, wanda daga cikin aikinsa har da tura tsofaffin ‘yan ta’adda karatu a kasashen ketare.
Kudirin ya ce za a cire 0.5% daga cikin kason jihohin Arewa maso gabas, sannan hukumomin TETFund da UBEC za su ba hukumar 1% daga kasonsu.
Tsohon Tauraron na Super Eagles, Obodo, ya fito bayan wasu 'yan sa'o'i a hannun Miyagun.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng