Mutanen da aka sace a wani masallaci a jihar Nasarawa sun samu ‘yanci

Mutanen da aka sace a wani masallaci a jihar Nasarawa sun samu ‘yanci

- An fito da mutanen da aka yi garkuwa da su a masallaci a Nasarawa

- Wannan mummunan lamarin dai ya auku ne a garin Gwargwada-Sabo

- Sai da aka tara kudi har Naira miliyan 8.5 kafin ‘yanuwansu su gansu

Dazu ne jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa mutane 17 da aka yi garkuwa da su a masallaci a Nasarawa a ranar Talata ta da wuce sun samu ‘yanci.

An yi sa’a, masu garkuwa da mutanen sun fito da jama’an da su ka dauke. Hakan na zuwa ne bayan iyalan kowane daga cikinsu sun tara N500, 000 sun biya fansa.

Jaridar ta ce jimillar abin da aka tara aka biya miyagun ya tashi a kan Naira miliyan 8.5.

KU KARANTA: An kai hari a Masallaci, an yanka Ladan

An fito da mutanen da aka tsare ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, 2020. An ajiye su a wani daji da ke hanyar Nicha zuwa Sabo a jihar Nasarawa.

Daga nan kowanensu ya nemi babur, aka kai shi gidansa bayan danginsa da sauran na-kusa da su sun sha wahala wajen tara kudin da za su biya a sake su.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa: “Da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya N1m domin a saki kowane wanda aka damke.”

KU KARANTA: An kama magidanci yana lalata a cikin Masallaci a Bauchi

Mutanen da aka sace a wani masallaci a jihar Nasarawa sun samu ‘yanci
Gwamnan Nasarawa da Shugaban kasa Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

“Bayan an shawo kansu, su ka amince kowa ya biya N500, 000.” Haka kuwa aka yi, mutane 17 su ka tattara, su ka hada masu Naira miliyan 8.5, kafin a sake su.

A makon jiya ne miyagu su ka kai farmaki a wani masallaci da ke garin Gwargwada-Sabo, karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa, su ka yi gaba da wasu.

Idan za ku tuna daga cikin wadannan Bayin Allah da aka sace har da wani ma’aikacin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Kaduna, mai suna Yusuf Shugar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng