Duniya labari: An kama magidanci yana lalata da yar shekaru 4 cikin Masallaci a Bauchi
Jama'ar unguwar titin Wunti (Wunti street), a jihar Bauchi, sun tsinci kawunansu cikin tashin hankali a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, sakamakon kama wani magidanci yana lalata da yarinya mai shekaru hudu a cikin masallacin unguwar.
Matasa da dattawan unguwar, ciki har da mata da kananan yara, sun taru a kofar masallacin, inda magidancin ya gamu da fushinsu, kafin zuwan jami'an 'yan sanda.
Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Bauchi, Sani Hamza Funtua, ya ziyarci unguwar da lamarin ya faru, inda ya tattauna da wasu matasa da dattawan unguwar kan lamarin.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa, Datti Datti, ya wallafa gajeren bidiyo a shafinsa na Facebook, lokacin da aka tsare magidancin a gaban Masallacin kafin zuwan 'yan sanda.
KARANTA WANNAN: Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu
A cewar wani matashi da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, "Da kusan sallar Azahar, wadanda suke a wajen masallacin suka rinka jin ihun yarinyar.
"Kasancewar Masallaci ne, babu wanda ya yi tunanin wani mummunan abu ke faruwa, a tunaninmu yarane suka shiga ciki, amma me zai kai mace cikin masallacin?
"Wannan ya sa muka shiga ciki don ganin abunda ke faruwa, cikin kaduwa da mamaki, muka taras da wani magidanci, ya gama yiwa yarinyar fyade, gaba daya jikinta jini ne.
"Wannan rashin imani ne, ya lalatawa yarinyar farjinta, jini kawai ke bin cinyoyinta, ta ci kukan azabar da take sha," a cewar matashin.
Da wakilin ya tuntubi wani magidanci a unguwar, shi ma da ya bukaci a sakaya sunansa, ya labarta cewa, "Bayan da aka ceci yarinyar daga hannun mutumin, an kaita asibiti.
"Yanzu haka tana asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, inda take samun kulawa daga likitoci, amma wannan rashin imanin har ina?
"Lokacin da aka kamashi, bana nan, amma an kirani a waya aka sanar da ni, da na iso, na taras mutanen unguwar suna kan dukansa, muka hanasu, don gudun aikata wani laifin.
"Mun sanar da jami'an tsaro, inda suka karaso, suka yi awon gaba dashi, yanzu haka yana ofishin CID, a nan Bauchi," a cewarsa
A lokacin da mutanen unguwar ke tuhumarsa kan dalilin da ya sa ya aikata wannan laifi, wani dattijo ya ce magidancin ya sanar da su cewa "Kungiyar asiri garemu, dole ta sa na yi hakan.
"Mu biyar ne na sani cikin kungiyar tamu a nan Bauchi, mun yanke shawarar bazama cikin unguwannin jihar, kuma kungiyar ce ta ce mana lallai sai a cikin Masallaci ne zamu yi fyaden."
Ko da suka tambayi mutumin kan labarin daga inda ya fito, ya shaida masu cewa shi dan asalin unguwar Yakubu Wanka ne dake cikin garin Bauchi.
Haka zalika ya shafe kwanaki biyar yana zuwa unguwar titin Wunti, har ya saba da yaran unguwar, saboda yana raba masu kudi da alawa.
Saboda sabon da yaran suka yi da shine, ya samu damar yaudarar yarinyar 'yar shekaru hudu, ya shigar da ita Masallacin ba tare da kowa ya gani ba.
Duk wani yunkuri na tuntubar jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Ahmad Wakil ya ci tura, har zuwa lokacin rubuta labarin nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng