Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17

Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17

- Ana tsakiyan Ibada, bata gari cikin al'umma sun yi aika-aika

- Masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa milyan hamsin, amma daga baya sun rage

- Har yanzu ba'a samu ceto wadanda aka sace daga hannunsu ba

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Masallaci kuma sun sace mutane 17 a unguwar Gwargwada-Sabo dake garin Gadabuke a jihar Nasarawa.

An tattaro cewa wadanda aka sace sun hada da wani ma'aikacin jami'ar Ahmadu Bello Zariya, mata 3 a wasu maza 13, a cewar rahoton Daily Trust.

Wani mazaunin unguwar mai suna Usman ya ce wannan abu ya faru ne daren Talata yayinda ake Sallan Isha'i.

"Yan bindigan na shigowa suka fara harbin kan mai uwa da wabi, yayinda sauran suka shiga cikin Masallacin sukayi awon gaba da su cikin daji," yace.

Limamin Masallacin da yaranshi kadai suka tsira.

Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17
Yan bindiga sun kai hari Masallaci a Nasarawa, sun yi awon gaba da Masallata 17
Asali: UGC

KU KARANTA: Don hana dalibai masu Hijabi shiga makaranta, an bankawa ofishin shugaban makaranta wuta

Iyalan wadanda aka sace sun samu tattaunawa da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci milyan daya-daya kan kowani mutum.

"Da farko sun bukaci milyan 50, amma da muka cigaba da tattaunawa da su, sai suka ce mu biya milyan kan kowani mutum," ya kara.

Duk yunkurin ji daga bakin kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ASP Rahman Nansel, ya ci tura.

DUBA NAN: Ku kwantar da hankulanku, ba za'a yi wahalan mai a Kano da wasu jihohin Arewa ba - IPMAN

A wani labarin da muka kawo muku, sa’o’i bayan gwamna Ahmadu Fintiri ya aika sakon gargadi zuwa ga bata garin da suka yi sace-sace a rumbunan ajiya a Adamawa, wasu da suka yi satan sun fara dawo da kayayyakin da suka sata domin tsiratar da kansu daga hukunci mai tsanani.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa gwamnan ya yi barazanar cewa zai rushe gidajen da aka samu kayayyakin satan a ciki

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel