Dan ta'adda ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)

Dan ta'adda ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)

Wani mamba a kungiyar ta'addanci da aka fi yi wa lakabi da 'right wing' ya kai hari a kan wani Masallaci da ke kasar Ingila.

Yayin harin, wanda aka kai daidai lokacin sallar La'asara, an yanki ladanin Masallaci a wuya.

Yanzu haka an rufe Masallacin yayin da jami'an tsaro suka yi nasarar kama wanda ya kai harin.

Wanda ya kai hari ya saci numfashin Musulman da suke shirin gudanar da sallar La'asar a Masallacin ranar Alhamis.

Ko a cikin shekarar da ta gabata sai da wani dan ta'adda ya kai hari wani Masallaci da e kasar Belgium, inda ya bude wuta a kan masallata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu.

Dan ta'addanci ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)
Dan ta'addanci ya kai hari Masallaci a London
Asali: Facebook

Dan ta'addanci ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)
Dan ta'addanci a hannun jami'an 'yan sanda
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng